An Ji Fashe Fashe a Iran, Gwamnati Ta Fitar da Sanarwa
- An ji ƙarar fashe-fashe guda biyu a tsibirin Qeshm da ke Kudancin Iran bayan dakarun ƙasar sun yi arangama da wasu abubuwan da aka bayyana a matsayin maƙiya
- Rahotanni sun ce fashe-fashen sun faru ne kusa da mashigar tekun Hormuz, yayin da dakarun ruwan Iran ke gudanar da wani samame
- Mahukuntan lardin Hormozgan sun ce ba a samu rahoton wani hari ko wata barna a tsibirin Qeshm da birnin Bandar Abbas ba, yayin da ake gudanar da bincike kan musabbabin lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tehran, Iran – An ji ƙarar fashe-fashe guda biyu a tsibirin Qeshm da ke lardin Hormozgan a Kudancin Iran a daren Alhamis, yayin da ake zargin dakarun ƙasar sun yi arangama da wasu abubuwan da suka bayyana a matsayin "maƙiya".
Kamfanin dillancin labarai na Tasnim da ke kusa da mahukuntan Iran ya ruwaito cewa fashe-fashen sun faru ne a kusa da mashigar tekun Hormuz.

Source: Getty Images
Anadolu ta nakalto majiyoyi masu masaniya da lamarin na cewa an ji fashe-fashen ne da misalin ƙarfe 9:40 na dare agogon ƙasar Iran.
Abin da ya faru a Qeshm
A cewar Tasnim, dakarun ruwan Iran sun yi wani samame kan abubuwan da aka bayyana a matsayin "maƙiya" a mashigar tekun Hormuz.
Majiyoyin sun ce za a sanar da sakamakon aikin da dakarun ruwan Iran suka gudanar cikin sa'o'i masu zuwa.
Sai dai mataimakin gwamnan lardin Hormozgan mai kula da harkokin siyasa, tsaro da zamantakewa, Ahmad Nafisi, ya ce ba a samu rahoton wani hari ko wani lamari na musamman a tsibirin Qeshm ko babban birnin lardin, Bandar Abbas ba.
Ya ce hukumomin da abin ya shafa suna gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin fashe-fashen.
Yunkurin sake buɗe Hormuz
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa Iran da Oman sun cimma fahimtar farko kan yarjejeniyar sake buɗe mashigar Hormuz na tsawon kwanaki 60.
Tashoshin yada labarai sun ruwaito cewa yarjejeniyar, wadda har yanzu ke buƙatar amincewar Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, na da nufin dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar.
A cewar rahotannin, jiragen ruwa da za su shiga mashigar za su bi wata hanya da ke kusa da Iran, yayin da waɗanda za su fita za su bi hanyar da ke kusa da Oman.

Source: Getty Images
Rahoton Gulf News ya ce ba za a karɓi kuɗin wucewa ko na wasu hidimomi daga jiragen ruwa ba, yayin da ƙasashen yankin za su iya shiga ayyukan kawar da nakiyoyi da sauran matakan fasaha.
China ta sa wa Amurka takunkumi
A wani labarin, mun ruwaito cewa China ta sanar da wasu matakan tattalin arziki kan Amurka, ciki har da takaita fitar da jirage marasa matuƙa zuwa Amurka da kuma hana hulɗa da wasu kamfanonin Amurka.
Matakin ya zo ne a matsayin martani ga wasu takunkuman da gwamnatin Amurka ta kakaba wa kamfanonin China bayan wasu zarge-zarge.
Hakan na faruwa ne yayin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin manyan ƙasashen biyu, duk da shirye-shiryen wata ziyara da ake sa ran shugaban China, Xi Jinping, zai kai Amurka.
Asali: Legit.ng

