Kwankwaso Ya Yi Magana kan Sabuwar Dokar NDC Ta Hana Sauya Sheka bayan Cin Zabe

Kwankwaso Ya Yi Magana kan Sabuwar Dokar NDC Ta Hana Sauya Sheka bayan Cin Zabe

  • Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tofa albarkacin bakinsa kan sabuwar dokar da jam'iyyar NDC ta bullo da ita
  • Dan takarar mataimakin shugaban kasar a zaben 2027 ya nuna cewa dokar abu ne wanda suka dade suna magana a kai
  • Dokar dai mai neman hana 'yan siyasa sauya sheka bayan cin zabe ba ta shafi Peter Obi da madugun na Kwankwasiyya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC a zaben 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan sabuwar dokar da jam'iyyar adawar ta bullo da ita.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya goyi bayan sabuwar dokar jam’iyyar NDC da za ta hana ’yan siyasa sauya sheƙa bayan sun ci zaɓe a karkashin inuwarta.

Kwankwaso ya goyi bayan sabuwar dokar NDC
Dan takarar mataimakin shugaban na ADC a zaben 2027, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa mai magana da yawun kungiyar Kwankwasiyya, Habibu Saleh Mohammed ne,ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Kara karanta wannan

NDC ta kafa sharadi ga yan takarar gwamna da na majalisu kafin mika sunaye ga INEC

NDC ta kawo sabon tsari

Jam’iyyar NDC dai ta bullo da wata sabuwar doka da za ta tilasta wa ’yan takararta sanya hannu kan takardar rantsuwa da ke tabbatar da cewa za su mika kujerunsu idan suka sauya sheka bayan sun ci zabe.

NDC ta ce sanya hannu kan wannan takarda zai zama sharadi kafin a tura sunayen ’yan takara zuwa hukumar INEC lokacin da za ta bude shafinta na karbar sunaye a ranar 26 ga watan Yunin 2026.

Shugaban NDC ya bayyana cewa manufar wannan mataki ita ce kare kuri’un jama’a, karfafa da’a a cikin jam’iyya da kuma dakile yawaitar sauya sheka bayan an ci zabe.

Sai dai, wannan tsari bai shafi dan takarar shugaban kasa, Peter Obi da mataimakinsa, Sanata Rabiu Kwankwaso ba.

Me Kwankwaso ya ce kan sabon tsarin?

Mai magana da yawun bakin na Kwankwasiyya ya ce sabon tsarin da NDC ta bullo da shi ya dace da abin da suka daɗe suna kira a kai, wato biyayya ga jam’iyya da mutunta ƙa’idojin dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ware rukunin 'yan bindigan da zai yi sulhu da su idan ya zama shugaban kasa a 2027

Habibu Saleh Mohammed, ya kuma bayyana iri ƙalubalen da Kwankwasiyya ta fuskanta a baya, sakamakon ficewar wasu manyan mambobinta ciki har da gwamna mai ci, inda suka koma wasu jam’iyyu.

“Abin da jam'iyyar ke ƙoƙarin yi shi ne kawai tilasta aiwatar da matsayar tsarin mulkin Najeriya. Kamar yadda abin yake, wannan shi ne ainihin abun da muke ta magana a kai."

- Habibu Saleh Mohammed

Kwankwaso ya goyi bayan jam'iyyar NDC
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron jam'iyyar NDC Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Ya tuna cewa ƙungiyar Kwankwasiyya ta fuskanci cikas a baya lokacin da wasu manyan jiga-jigai suka fita daga cikinta, ciki har da gwamna mai ci kuma tsohon mataimakin shugaban ƙungiyar, Abdullahi Umar Ganduje.

Yaron Kwankwaso ya samu takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa yaron Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wato Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso, ya samu tikitin takarar mataimakin gwamnan Kano na jam'iyyar NDC.

Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar NDC, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya zabi Mustapa Rabiu Kwankwaso a matsayin abokin takararsa a zaben 2027.

Mustapha Rabiu Kwankwaso dai tsohon kwamishinan matasa da wasanni ne a gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng