Shettima Zai Bar Ofis na tsawon Makonni 2, Ya Aika Muhimmin Sako ga Ƴan Najeriya

Shettima Zai Bar Ofis na tsawon Makonni 2, Ya Aika Muhimmin Sako ga Ƴan Najeriya

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya fara hutun mako biyu na farko tun bayan hawansa mulki a watan Mayun shekarar 2023
  • Fadar shugaban ƙasa ta ce Kashim Shettima zai yi amfani da hutun wajen yin nazari, tunani da ƙara ƙwarewa domin inganta ayyukansa
  • Sanarwar ta bayyana cewa mataimakin Shettima zai koma bakin aiki bayan hutun tare da sabon kuzari na ci gaba da aiwatar da shirin Renewed Hope

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja – Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya fara hutun mako biyu bayan samun amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Kashim Shettima ya fara hutun makonni 2
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima da ya fara hutun makonni 2. Hoto: stanleynkwocha_/X
Source: Facebook

Stanley Nkwocha, ya fitar da wannan sanarwar ne a shafinsa na X a ranar Alhamis, 6 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

2027: Dan takarar shugaban kasa ya hakura d shiga zabe, ya bi bayan Tinubu

Kashim Shettima ya tafi hutu

Sanarwar ta bayyana cewa wannan ne karon farko da Shettima ya tafi hutu tun bayan rantsar da shi a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

A cewar sanarwar, hutun zai bai wa mataimakin shugaban ƙasar damar mayar da hankali wajen yin nazari, tunani da ƙara faɗaɗa iliminsa domin ƙarfafa ƙwarewarsa wajen ci gaba da yi wa Najeriya hidima.

Sanarwar ta ce:

"A lokacin hutun, mataimakin shugaban ƙasa zai ba da lokaci wajen yin nazari, tunani da sabunta iliminsa domin ƙarfafa ƙwarewarsa wajen ci gaba da yi wa ƙasa hidima."

Ta ƙara da cewa hutun zai kuma ba Shettima damar sake duba shirye-shiryen gwamnatin tarayya da ke gudana, tare da zurfafa fahimtarsa kan sabbin manufofin cikin gida da na ƙasa da ƙasa.

Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa hakan zai taimaka masa wajen shirya kansa domin ƙarin nauyin da ke gabansa yayin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da aiwatar da ajandar Renewed Hope.

Kara karanta wannan

Bayani kan ƙarin albashi da Tinubu ya yi wa ƙanana da manyan sojojin Najeriya

Ayyukan da Shettima ke jagoranta

Fadar shugaban ƙasa ta ce tun bayan hawansa mulki, Shettima ya ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen jagoranci da sa ido kan muhimman shirye-shiryen gwamnati.

Sanarwar ta ce:

"Tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayun 2023, mataimakin shugaban ƙasa ya kasance yana jagoranci da sa ido kan muhimman shirye-shiryen gwamnati, musamman a fannonin bunƙasa tattalin arziki, wadatar abinci, ayyukan jin ƙai, sauyin fasahar zamani, samar da ayyukan yi da haɗin gwiwar yankuna."

Har ila yau, Shettima ne ke jagorantar zaman Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (National Economic Council), wadda ta haɗa gwamnonin jihohi 36, gwamnan Babban Bankin Najeriya da sauran manyan jami'an gwamnati domin tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arzikin ƙasa.

Baya ga haka, ya wakilci Shugaba Tinubu a tarurruka da dama na ƙasa da ƙasa, inda ya gabatar da matsayar Najeriya kan batutuwan tattalin arziki, zaman lafiya, tsaro, sauyin yanayi, zuba jari da ci gaba mai ɗorewa.

Kara karanta wannan

Rikici ya danno cikin kungiyar goyon bayan Obi da Kwankwaso gabanin 2027

An ce Kashim Shettima zai dawo hutu bayan makonni 2
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yana sauko wa daga jirgin sama. Hoto: stanleynkwocha_/X
Source: Facebook

Lokacin da zai Shettima koma bakin aiki

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Shettima na nan daram kan jajircewarsa wajen yi wa ƙasa hidima da kuma mara wa Shugaba Bola Tinubu baya wajen aiwatar da manufofin gwamnati.

Sanarwar ta ce:

"Mataimakin shugaban ƙasar zai koma bakin aiki bayan kammala hutun mako biyun tare da sabuwar himma da ƙwazo wajen ci gaba da yi wa ƙasa hidima."

An bayyana cewa hutun zai ƙare ne bayan mako biyu, inda ake sa ran Shettima zai dawo domin ci gaba da gudanar da ayyukansa a gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com