Yau ake Gudanar da Zabe a Kano, Ekiti da Wasu Jihohin Najeriya
- An kammala shirye-shiryen zaben gwamna a Ekiti da zabukan cike gurbi a jihohi shida, inda ’yan takara 37 ke neman kujeru bakwai
- Hukumar zabe ta kasa wato NEC ta raba kayayyakin zabe, yayin da hukumomin tsaro suka gano wurare 460 masu bukatar kulawa
- Kungiyar Yiaga Africa ta yi gargadi cewa sayen kuri’u na iya zama babbar barazana ga sahihancin zaben da za a gudanar a yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bayan kammala yakin neman zabe da kuma rabon kayayyakin zabe da INEC ta gudanar, an shirya tsaf domin zaben gwamnan Ekiti .
Haka zalika za a gudanar da zaben cike gurbi na kujerun sanata hudu, kujera daya ta majalisar wakilai da kuma kujera daya ta majalisar dokokin Jiha a jihohi shida.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa za a gudanar da zabukan sanata a jihohin Enugu, Ondo, Nasarawa da Rivers, yayin da za a gudanar da zabukan cike gurbi na majalisar wakilai da na majalisar dokokin jiha a Kano da Kebbi.
Shirin da 'yan sanda suka yi
'Yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun gargadi masu niyyar tada zaune-tsaye da masu magudin zabe, tare da yin alkawarin hukunta su ba tare da sassauci ba.
Kwamishinan ’yan sanda da aka tura domin zaben gwamnan Ekiti, Abayomi Shogunle, ya bayyana cewa ba za a amince da sayen kuri’u ba.
Shogunle ya ce an gano wurare 460 masu yiwuwar rikici a cikin kananan hukumomi 16 na jihar, kuma an kara tura jami’an tsaro zuwa wuraren domin hana karya doka da oda.
INEC ta raba kayan zabe
A Ekiti, hukumar zaben ta fara raba kayayyakin zabe masu muhimmanci zuwa dukkan kananan hukumomi 16 na jihar.
An fara aikin da misalin karfe 1:25 na dare a ofishin CBN da ke Ado-Ekiti, karkashin tsauraran matakan tsaro daga ’yan sanda da jami’an NSCDC.
An fara rabon ne da kananan hukumomin da suka fi nisa da babban birnin jihar, ciki har da Ilejemeje, Ayekire, Ido-Osi, Ijero, Ikole, Ekiti East da Emure.

Source: Facebook
Korafin kan sayen kuri’u
A gefe guda, kungiyar Yiaga Africa ta bayyana cewa sayen kuri’u ne babbar barazana ga sahihancin zaben gwamnan jihar Ekiti da za a gudanar ranar Asabar,
Shugabar tawagar masu sa ido ta Yiaga Africa a Ekiti, Aisha Abdullahi, ta ce duk da cewa shirye-shiryen zaben sun gudana cikin kwanciyar hankali, sayen kuri’u na iya lalata tsarin zaben.
'APC ta gaza a Ekiti' ADC
Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban jam’iyyar ADC na kasa, David Mark, da tsohon gwamnan jihar Osun kuma sakataren jam’iyyar na kasa, Rauf Aregbesola, sun soki gwamnatin APC a Ekiti.
Sun bayyana cewa ta gaza wajen biyan bukatun jama’a kuma ba za ta iya tsira ba idan aka gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci ba.
Dukkan shugabannin biyu sun bayyana hakan ne a wani gangamin yakin neman zabe a Ado-Ekiti, inda dubban magoya baya suka hallara gabanin zaben gwamnan.

Source: Facebook
APC na fafatawa da LP a Kano
A Jihar Kano, ’yan takara uku ne ke neman wakiltar mazabar tarayya ta Dawakin Kudu/Warawa a Majalisar Wakilai.
Punch ta wallafa cewa za a gudanar da zaben ne domin cike gurbin da rasuwar tsohon dan majalisar, Muhammad Hassan, ta haifar.
’Yan takarar da INEC ta tantance sun hada da Rabi’u Shuaibu na APC, Lawan Garba Haruna na APM da Abubakar Yahaya Muhammad na LP.
APC za ta iya nasara a Ekiti
A wani labarin, Legit Hausa ta hada muku rahoto na musamman game da abubuwan da za su iya sanya APC samun nasara a zaben Ekiti.
Kasancewar gwamnan jihar mai ci, Biodun Abayomi Oyebanji dan jam'iyyar APC mai mulki ne ya kasa wa jam'iyyar damar samun nasara.
Haka zalika goyon bayan da Biodun Abayomi Oyebanji ya samu daga wajen tsofaffin gwamnonin Ekiti irinsu Ayo Fayose ya nuna alamun zai iya lashe zaben.
Asali: Legit.ng


