An Fitar da Jerin Kasashe 50 da Trump Ya Laftawa Wasu Kudi, ciki har da Najeriya
- Gwamnatin Amurka ta mayar da shirin biyan lamunin biza na dala 20,000 dindindin ga matafiya daga kasashe 50 da suka hada da Najeriya
- Shirin zai shafi wasu masu neman bizar kasuwanci da yawon bude ido, inda za a mayar musu da kudin idan sun bi sharuddan zama a Amurka
- Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce biyan lamunin ba ya tabbatar da samun biza, kuma za a biya ne kawai idan jami'in ofishin jakadanci ya bayar da umarni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington DC – Gwamnatin Amurka ta sanar da mayar da shirin biyan lamunin biza na dala 20,000 dindindin ga matafiya daga kasashe 50, ciki har da Najeriya da wasu kasashen Afirka 29.
Sabuwar dokar za ta shafi wasu masu neman bizar B1/B2 ta kasuwanci da yawon bude ido, inda jami'in ofishin jakadanci zai iya umartar su da su biya lamunin kafin a ba su bizar shiga kasar.

Source: Getty Images
Punch ta rahoto cewa Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a ranar Juma'a, tana mai cewa shirin zai taimaka wajen tabbatar da bin dokokin shige da fice.
Yadda shirin lamunin biza zai gudana
A cewar gwamnatin Amurka, duk matafiyin da ya bi sharudan bizar kuma ya fice daga kasar kafin wa'adin zamansa ya cika, za a mayar masa da kudin lamunin.
Ma'aikatar ta ce jami'an jakadanci na iya bukatar masu neman biza su biya lamunin da zai kai dala 20,000 kafin a ba su izinin tafiya.
Ta kara da cewa shirin gwajin da aka fara a shekarar 2025 ya nuna cewa tsarin yana taimakawa wajen tabbatar da cewa masu biza suna bin dokokin shige da fice na Amurka.
Jerin kasashen da abin ya shafa
Vanguard ta wallafa cewa sabuwar dokar ta shafi kasashe 50 a fadin duniya yayin da guda 30 suka kasance daga nahiyar Afrika;
- Algeria
- Angola
- Antigua and Barbuda
- Bangladesh
- Benin
- Bhutan
- Botswana
- Burundi
- Cabo Verde
- Cambodia
- Central African Republic
- Côte d'Ivoire
- Cuba
- Djibouti
- Dominica
- Ethiopia
- Fiji
- Gabon
- The Gambia
- Georgia
- Grenada
- Guinea
- Guinea-Bissau
- Kyrgyz Republic
- Lesotho
- Malawi
- Mauritania
- Mauritius
- Mongolia
- Mozambique
- Namibia
- Nepal
- Nicaragua
- Nigeria
- Papua New Guinea
- São Tomé and Príncipe
- Senegal
- Seychelles
- Tajikistan
- Tanzania
- Togo
- Tonga
- Tunisia
- Turkmenistan
- Tuvalu
- Uganda
- Vanuatu
- Venezuela
- Zambia
- Zimbabwe

Source: Facebook
Jirgin yaki ya yi hatsari a Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani jirgin yakin F-35B na rundunar sojin ruwa ta Amurka ya yi hatsari tare da kama wa da wuta a yankin jihar California.
Matukin jirgin ya samu damar amfani da na'urar ceto kafin jirgin ya fadi, kuma an kai shi asibiti inda likitoci suka tabbatar cewa raunukan da ya samu ba su da hadarin rasa rai.
Jami'an kashe gobara sun garzaya wurin domin kashe wutar da ta tashi bayan hatsarin, yayin da ake ci gaba da binciken musabbabin afkuwar lamarin.
Asali: Legit.ng

