An Fallasa Shirin Shawo kan Talaka da Shinkafa da Taliya a Zaben Gwamnan Ekiti

An Fallasa Shirin Shawo kan Talaka da Shinkafa da Taliya a Zaben Gwamnan Ekiti

  • Rahoto ya nuna cewa hukumar zabe ta kasa (INEC) ta yi magana game da shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti da za a yi a 2026
  • Kungiyar Yiaga mai saka ido a kan harkokin zabe ta yi zargin cewa wasu 'yan siyasa sun fara shirye-shiryen raba shinkafa da taliya ga masu zabe
  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ya bayyana cewa an samu karin masu kada kuri'a fiye da yadda aka samu a jihar a zaben 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum

Jihar Ekiti - Daya daga cikin jagororin kungiyar Yiaga Africa, Safiya Bichi, ta ce zaɓen Ekiti zai iya jawo gasa a siyasar Najeriya idan mutane da yawa suka fito kaɗa kuri’a a ranar Asabar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar INEC ta sanar da cewa shirye-shiryen zaben gwamna a jihar Ekiti na ranar 20 ga Yunin 2026 sun kankama yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ware rukunin 'yan bindigan da zai yi sulhu da su idan ya zama shugaban kasa a 2027

Wani mutum na kada kuri'a a zabe a Abuja
Yadda wani mutum ya kada kuri'a a akwatin zabe a Najeriya. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Safiya Bichi ta bayyana haka ne a wata hira da aka yi da ita a tashar Channels Television a ranar Alhamis, 18 ga watan Yunin 2026.

Maganar raba shinkafa da taliya

A bayanin da ta yi, Bichi ta yi zargin cewa ana shirin raba kayan abinci gabanin zaɓen domin jan hankalin talakawa masu kada kuri'a.

Ta ce:

"Shinkafa, kuɗi, taliyar Indomie, da duk irin waɗannan kayan abinci da ake rabawa, ana mika su ne ana alkawura gabanin zaɓen."

Rahotanni sun nuna cewa ta kuma yi magana kan maganar da ke yawo a bakin mutane cewa kada kuri'a bata da wani amfani a kasar nan.

“Akwai kuma maganar da ta shahara a Najeriya, ba a Ekiti kaɗai ba, cewa kuri’a ba ta da amfani, amma muna gaya wa matasa cewa kuri’arsu na da amfani.
“Idan ba ta da amfani, babu wanda zai tsaya sayen ta, kuma waɗannan su ne kalmomin da muke amfani da su domin ƙarfafawa da jan hankalin ‘yan ƙasa su shiga tsarin zaɓe,”

Kara karanta wannan

Farashin man fetur zai ruguzo a Najeriya bayan kammala yakin Iran da Amurka

Bayanin hukumar zabe ta kasa

The Cable ta wallafa cewa bayanin Safiya Bichi ya zo ne yayin da INEC ke shirin gudanar da zaɓen gwamna a Ekiti a ranar 20 ga Yuni, 2026.

Shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan, ya bayyana cewa hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓen.

Shugaban hukumar zabe ta kasa a Abuja
Shugaban INEC, Joash Amupitan da abokin aikin shi a ofis. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Ya tabbatar wa masu zaɓe, jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki cewa an kammala duk shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya, gaskiya da sahihanci a zaben.

INEC ta kuma bayyana cewa yawan masu rajistar zaɓe a jihar Ekiti ya ƙaru daga 987,647 a 2023 zuwa 1,059,360 a 2026.

Ga wani sashe na bayanin da Yiaga ta yi:

Zabukan da za a yi a ranar Asabar

A wani labarin, mun kawo muku cewa hukumar zabe ta kasa ta sanar da cewa ta kammala shirye-shiryen gudanar da zabuka a jihohi biyar.

Bayanin da hukumar ta fitar ya nuna cewa za a gudanar da zaben gwamna a Ekiti da zaben cike gurbi a wasu jihohi hudu a ranar 20 ga Yunin 2026.

Sanarwar da hukumar INEC ta fitar ya nuna cewa jihohin da za gudanar da zabukan sun hada da Kano, Kebbi, Ekiti, Enugu da Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng