Sojojin Isra'ila Sun Bijirewa Umarnin Donald Trump, Sun Kaddamar da Hare Hare
- Hare-haren Isra'ila sun kashe akalla Falasɗinawa 26 a ƙarshen mako, duk da sabon shirin ci gaba da tsagaita wuta a Gaza
- Hamas ta amince da tsarin sulhun, amma gwamnatin Isra'ila ta ce har yanzu tana da damuwa kan tsaron ƙasarta
- Masana sun yi gargaɗin cewa ci gaba da kai hare-hare na iya rusa shirin zaman lafiya tare da ƙara ta'azzara matsalar jin kai a Gaza
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Isra'ila - Hare-haren sojojin Isra'ila a Zirin Gaza sun ƙaru tun bayan sanar da shirin fara mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a makon da ya gabata, lamarin da ya jefa makomar sulhun cikin rashin tabbas.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana amincewar Hamas da sabon tsarin sulhun a matsayin babban ci gaba wajen samar da tsaro da zaman lafiya.

Source: Getty Images
Isra'ila ta nuna damuwa kan shirin Trump
Sai dai a Gaza, hare-haren Isra'ila sun ci gaba, inda aka kashe akalla Falasɗinawa 26 a ƙarshen mako, ciki har da mata da yara, in ji rahoton Aljazeera.
Ko da yake Hamas ta amince da wani tsari na ajiye makamai a matakai, gwamnatin Isra'ila ta ce har yanzu tana da "matsananciyar damuwa" kan batun tsaron ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan siyasar Isra'ila sun nuna adawa da yarjejeniyar, suna neman a kwace dukkan makaman Hamas kafin sojojin Isra'ila su janye daga Gaza.
Kakakin ofishin Firaminista Benjamin Netanyahu, Doron Spielman, ya ce sojojin Isra'ila ba za su fice daga Gaza ba har sai an tabbatar da cewa Hamas ba ta da makamai gaba ɗaya.
Masana sun yi gargaɗi kan harin Isra'ila
Masanin siyasar Falasɗinu da ke Gaza, Eyad al-Qarra, ya ce janye daga yarjejeniyar zai iya zama babban haɗari ga Hamas da sauran ƙungiyoyin Falasɗinawa.
Ya ce ci gaba da bin yarjejeniyar zai hana Isra'ila samun hujjar faɗaɗa yaƙin da take yi a Gaza.
A cewarsa, bai kamata ƙungiyoyin Falasɗinawa su ba Isra'ila wata dama da za ta sa a ɗora musu alhakin rushewar shirin sulhu ba.
Rikici kan makamai da mulkin Gaza
Rahotanni daga Isra'ila sun ce gwamnati na neman a miƙa makaman Hamas ga wata ƙasa ta Yamma, tare da hana kowace ƙungiyar Falasɗinawa shiga aikin kwace makaman.

Source: Getty Images
Haka kuma, sojojin Isra'ila sun ce ba za su janye daga wani yanki da ake kira Yellow Line, wanda ya mamaye kusan kashi 52 cikin 100 na Zirin Gaza ba.
A gefe guda, sabon tsarin sulhun ya tanadi kafa wata gwamnatin ƙwararru mai cin gashin kanta domin kula da harkokin farar hula da sake gina Gaza bayan yaƙin.
Sai dai masana sun yi gargadin cewa idan Isra'ila ta ci gaba da gudanar da ayyukan soji ba tare da ƙuntatawa ba, duk wata gwamnatin Falasɗinawa da za a kafa ba za ta iya gudanar da aikinta yadda ya kamata ba.
Isra''ila ta kai hare hare Gaza
A wani labari, mun ruwaito cewa, Isra'ila ta kai sababbin hare-haren sama a yankunan Zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa biyu.
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun afku ne duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani aka cimma a bara, yayin da rikicin ke ci gaba da tsananta.
Hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce sama da mutane miliyan 1.4 a Gaza na ci gaba da fuskantar matsananciyar yunwa da ƙarancin abinci duk da yarjejeniyar.
Asali: Legit.ng


