'Yan Takara 6 Mafi Yawan Shekaru da za Su Fafata a Zaben Gwamnan Ekiti
- 'Yan takarar gwamnan shida masu shekaru tsakanin 61 zuwa 67 sun bayyana a matsayin manyan masu takara a zaɓen gwamnan Jihar Ekiti
- Rahoto ya ce an bayyana ɗan takarar Jam’iyyar LP, Farfesa Oyebanji Olajuyin, a matsayin mafi tsufa a cikin takarar yana da shekaru 67
- Waɗannan tsofaffin 'yan siyasa da suke takara suna da tarihin aiki da ya shafi ilimi, diflomasiyya, hidimar gwamnati, kasuwanci da siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ekiti - Yayin da Jihar Ekiti ke shirin gudanar da zaɓen gwamna a ranar 20 ga Yuni, 2026, hankali ya karkata kan shekarun wadanda za su fafata.
A cikin 'yan takara, akwai ƙwararrun ‘yan siyasa masu shekaru da dama da gogewar aiki na shekaru da ke ci gaba da yin tasiri a zaben jihar.

Source: Facebook
A wannan rahoton, mun kawo muku jerin 'yan takara shida mafi yawan shekaru da za su fafata a zaben gwamna da za a yi a jihar Ekiti.
Bisa bayanan da hukumar zaɓe ta INEC ta fitar, akwai ‘yan takara shida masu shekaru 61 zuwa sama da ke neman kujerar shugabancin jihar.
Tsofaffin ‘yan takara a zaben gwamnan Ekiti
1. Farfesa Oyebanji Olajuyin (LP)
Dan shekaru 67, Farfesa Oyebanji Olajuyin shi ne mafi tsufa a cikin takarar. Likita ne, malami kuma mai kula da harkokin kiwon lafiya daga Ikere-Ekiti, wanda ya yi suna a fannin likitanci da ilimi mai zurfi.
Punch ta wallafa cewa Olajuyin da ke wakiltar LP na yin kamfen ne kan inganta kiwon lafiya, habaka ilimi, shugabanci na gaskiya da samawa ɗan Adam walwala.

Source: Facebook
Magoya bayansa na nuna tarihinsa na ilimi a matsayin hujjar ƙwarewarsa wajen tafiyar da cibiyoyin gwamnati yadda ya kamata.
2. Bejide Oluwadare Patrick (ADC)

Kara karanta wannan
Bincike: 'Yan bindiga ne suka mika gawar Janar Rabe hannu da hannu? Gaskiya ta fito
Rahoton Daily Trust ta wallafa cewa cewa dan takarar jam’iyyar adawa ta ADC, Oluwadare Patrick Bejide, ya shiga takarar yana da shekaru 66.
Bejide ya kasance tsohon jami’in diflomasiyya, ma’aikacin gwamnati kuma ɗan siyasa kuma yana da ƙwarewa mai yawa a harkokin mulki da shugabanci.

Source: Twitter
3. Anifowoshe Joseph Olanrewaju (APM)
Joseph Olanrewaju Anifowoshe, mai shekaru 65, ya kasance daga cikin ‘yan takarar gwamna da ke neman kujera a ƙarƙashin jam’iyyar APM.
Gwamnatin jihar ta wallafa cewa yana daga cikin tsofaffin da ke da alaƙa da takarar kafin ya janye tare da nuna goyon bayansa ga gwamnan da ke kan mulki.

Source: Facebook
4. Omotosho Mathew Olu (AA)
INEC ta sanar a shafinta cewa Omotosho Mathew Olu na jam’iyyar AA yana da shekaru 64 a halin yanzu da za a fafata da shi a zaben Ekiti.
Takarar shi ta ƙara nuna yawan tsofaffin ‘yan siyasa da ke ƙoƙarin ci gaba da kasancewa cikin harkokin mulki da shugabanci.

Source: Facebook
5. Wole Oluyede (PDP)
The Cable ta rahoto cewa Wole Oluyede mai shekara 61 ya fito a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP kafin a cire jam’iyyar sakamakon rikice-rikicen cikin gida da ƙalubalen shari’a.

Kara karanta wannan
1959 zuwa 2026: Lokuta 5 da Hausawa da Ibo suka haɗu a siyasance kafin tafiyar OK a NDC
Duk da wannan koma baya, shigarsa tun farkon matakan zaɓe ya tabbatar da matsayinsa a cikin fitattun wadanda suka nemi takara.

Source: Facebook
6. Olusegun Ayodele Osinkolu (YPP).
Legit ta wallafa cewa na karshe daga cikin 'yan takarar shi ne Olusegun Ayodele Osinkolu na jam’iyyar YPP mai shekara 61 da haihuwa.
Takarar shi ta nuna ƙudurin ƙananan jam’iyyu na ƙalubalantar manya a siyasa da gabatar da damar zaben mutane daban-daban ga masu zaɓe.

Source: Facebook
Bayanin Yiaga kan zaben Ekiti
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Yiaga Africa ta yi magana kan zaben da ake shirin gudanarwa a jihar Ekiti a ranar 20 ga Yunin 2026.
Jami'ar kungiyar, Safiya Bichi ta bayyana cewa an tanadi shinkafa, taliya, kudi da sauran kayayyaki domin shawo kan talakawa.
Ta yi kira ga mutanen jihar Ekiti da sauran jihohi da su yi watsi da batun cewa kada kuri'a ba shi da wani amfani a harkokin zabe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
