Magana Ta Kare, An Shirya Mika Kudirin Kirkiro Yan Sandan Jihohi ga Shugaba Tinubu

Magana Ta Kare, An Shirya Mika Kudirin Kirkiro Yan Sandan Jihohi ga Shugaba Tinubu

  • Kwamitin Shugaban Kasa kan Dokar Tsarin Aikin 'Yan Sanda ya ce zai mika kudirin ga Shugaban Kasa, Bola Tinubu ranar 3 ga Satumba, 2026
  • Shugaban kwamitin kuma shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya ce za a fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki kafin a gabatar da kudirin
  • Kwamitin ya bukaci 'yan Najeriya da kungiyoyi farren hula su gabatar da takardun shawarwarinsu a lokacin tattaunawa kan kudirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kwamitin Shugaban Kasa kan Kudirin Dokar Tsarin Aikin 'Yan Sanda ya sanar da shirinsa na tattaunawa mai zurfi kafin mika kudirin ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kwamitin ya bayyana cewa zai gabatar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kunshin kudirin dokar kirkiro rundunar yan sandan jihohi a ranar 3 ga watan Satumba, 2026.

Kara karanta wannan

Keyamo ya gano wanda zai ci zaben 2027 tsakanin Tinubu, Obi da Atiku

Gbaja.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila yana tsakiyar aiki a ofis a Aso Rock Hoto: Femi Gbajabiamila
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta rahoto cewa shugaban kwamitin kuma Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan yau Litinin, 3 ga watan Agusta, 2027.

Yayin da kwamitin yake wa manema labarai bayani kan halin da ake ciki a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, Gbajabiamila ya ce za a bai wa yan Najeriya damar ba da shawarwari.

Matakin da za a dauka kafin a gabatar da kudirin

Femi Gbaj"abiamila ya bayyana cewa kafin a mika kudirin ga Shugaba Tinubu, za a gudanar da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan daftarin da aka tsara game da rundunar yan sandan jihohi.

Ya ce manufar hakan ita ce tabbatar da cewa an samu ra'ayoyi daga bangarori daban-daban kafin a dauki matakin karshe, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

An bukaci jama'a su gabatar da shawarwari

Kwamitin ya kuma bukaci 'yan Najeriya, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki su gabatar da takardun shawarwari, bayanan matsayinsu da kuma hanyoyin da suke ganin za su taimaka wajen inganta kudirin.

Kara karanta wannan

Atiku ya kalubalanci Tinubu kan sayo motocin alfarma a kan N15.13bn

A cewar Femi Gbajabiamila, shawarwarin za su bai wa jama'a damar nazarin ainihin tanade-tanaden kudirin, matakan kariya da aka tanada, tsarin samar da kudade da kuma yadda za a aiwatar da sauye-sauyen da dokar za ta kunsa.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana rattaba hannu kan kudirin doka a fadar Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ya bayyana cewa 'yan Najeriya za su iya bayar da gudummawa da shawarwari kai tsaye wajen tsara dokar ta hanyar fura takardu ta shafin yanar gizo (nationalpolicingbill.com).

Majalisa shari'a ta ja hankali kan kudirin

A wani rahoton na daban, kun ji cewa Majalisar Koli ta Shari'ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta bada shawara kan gyaran kundin tsarin mulki game da kafa 'yan sandan jihohi.

A wata sanarwa da Sakatare Janar na majalisar, Nafiu Baba Ahmad, ya fitar, SCSN ta ce ta na bibiyar muhawarar da ake yi da kuma matakan da ake dauka kan batun kafa 'yan sandan jihohi.

Majalisar ta bukaci shugaban kasa, Majalisar tarayya da sauran masu ruwa da tsaki su kammala cikakkiyar tuntuba da 'yan Najeriya tare da magance damuwar jama'a kafin ci gaba aiwatar da kudirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262