Ekiti 2026: Manyan Laifuffukan Zabe a Najeriya da Hukuncin da Doka Ta Tanada

Ekiti 2026: Manyan Laifuffukan Zabe a Najeriya da Hukuncin da Doka Ta Tanada

Abuja – A tsarin dimokuradiyya, kada kuri'a ce hanyar da 'yan kasa ke zabar shugabannin da suke so, Najeriya ta tanadi dokoki masu tsauri domin kare tsarin zabe daga masu son yin magudi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dukkan wadannan dokoki suna cikin Dokar Zabe ta 2022, wacce ta amince da hukuncin tarar kudi ko zaman gidan yari, ko duka biyun ga duk wanda ya saba doka.

Yayin da ake shirin zaben Anambra, an jero manyan laifuffukan zaben a Najeriya da hukunce-hukunce su.
Hoton jami'ar hukumar INEC yayin da take tantance mai kada kuri'a a lokacin zabe. Hoto: @inecnigeria.
Source: Twitter

Laifuffukan zabe da hukuncinsu a Najeriya

Rahoton hukumar INEC ya nuna cewa laifuffukan zabe suna da hadari sosai ga tsarin dimokuraɗiyya, saboda suna kuma rage amincewar jama’a ga sakamakon zabe.

Saboda haka ne hukumar INEC da hukumomin tsaro ke yawan jan hankalin ‘yan kasa su guji aikata wadannan laifuffukan zaben da ke iya jefa su gidan yari na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Battujo: Kotu ta yanke wa mahaifiyar ƙasurgumin dan bindiga da 'yar'uwarsa hukunci

Legit Hausa ta duba wasu daga cikin tanade-tanaden dokar zabe yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnan Ekiti.

1. Laifin rijistar zabe sau 2 ko jabun katin zabe

Sashe na 114 na Dokar Zabe ya fayyace laifuffukan da suka shafi rijistar masu kada kuri’a, kamar yadda Legit Hausa ta gani a shafin intanet na ofishin lauyoyi na M.A Banire & Associates.

Wadannan laifuffuka sun haɗa da yin rijista fiye da sau ɗaya, yin jabun katin zabe, amfani da sunan jami’in rijista domin yin magudi, da kuma yin rijista da sunan wani mutum.

Doka ta ce duk wanda aka kama yana da hannu a irin wannan laifi zai fuskanci hukuncin tarar N1,000,000 ko zaman gidan yari na watanni 12 ko duka biyun.

Hakan na nufin cewa idan mutum ya taimaka wajen yin wannan laifi, ba lallai sai shi ne ya yi da kansa ba, to doka za ta hukunta shi kamar wanda ya aikata da hannunsa.

2. Jabun takardun takara ko sakomakon zabe

Sashe na 115 ya nuna irin laifuffukan da dan takara zai iya aikatawa wajen neman mukami. Wadannan sun haɗa da buga jabun takardar neman takara, takardar sakamako, ko takardar kada kuri’a, da kuma lalata ko mallakar takardar kuri’a ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

2026: Manyan abubuwa 3 da za su iya kawo wa APC cikas a zaben gwamnan Ekiti

Wanda aka samu da laifi a wannan sashe zai fuskanci tara ta N50,000,000 ko zaman gidan yari na shekaru 10 ko duka biyun.

Hukuncin yana da tsauri saboda yana shafar gaskiya da amincin sakamakon zabe gaba ɗaya.

Hukumar INEC ta gargadi 'yan Najeriya game da illar karya dokokin zabe
Sabon shugaban INEC, Joash Amupitan, ya na jawabi a ofishin hukumar a Abuja. Hoto: @inecnigeria.
Source: Twitter

3. Haddasa tarzoma a taron siyasa

Sashe na 116 na Dokar Zabe ya haramta duk wanda zai yi ko ya haddasa tarzoma a wajen taron siyasa, musamman idan manufarsa ita ce tayar da zaune tsaye ko hana gudanuwar taron.

Doka ta ce duk wanda aka kama yana da makami ko abin tayar da hankali a wajen taron siyasa zai fuskanci hukuncin tara na N500,000 ko zaman gidan yari na watanni 12 ko duka biyun.

Wannan sashe ya ba da kariya a lokacin yakin neman zabe, inda wasu jam’iyyun ke amfani da ‘yan daba don hana abokan hamayya gudanar da taruka cikin lumana.

4. Amfani da katin zabe na wani

Sashe na 117 ya tanadi hukunci ga duk wanda ke amfani da katin zabe na wani mutum ko wanda yake da katin zabe fiye da guda daya.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin jihar Ekiti daga 1999 zuwa yau yayin da ake shirin sabon zabe a 2026

Hakanan, duk wanda ya sayar da katin zabe, ya siya, ko ya karɓa ba bisa doka ba, to ya aikata babban laifi a karkashin wannan sashe.

Hukuncin irin wannan laifi shi ne tara har ta N1,000,000 ko zaman gidan yari na watanni 12 ko duka biyun.

INEC ta sha gargadin jama’a da su daina ba da katin zabensu ga wasu, ko karɓar na wani, saboda hakan yana iya kai su ga daurin shekara guda.

5. Jefa kuri’a sau 2 ko sojan gona da wani

Sashe na 119 ya haramta kada kuri’a fiye da sau ɗaya a zabe guda, ko yin amfani da sunan wani dan kasa domin kada kuri’a.

Wanda ya aikata haka zai fuskanci tara ta N500,000 ko zaman gidan yari na watanni 12 ko duka biyun.

Wannan doka tana tabbatar da adalci wajen zabe, saboda tana hana mutane suyi amfani da katin jabu ko su kada kuri’a a wurare fiye da daya.

INEC ta bullo da amfani da na'urar BVAS domin tabbatar da cewa kowane mutum ya kada kuri’a sau ɗaya kawai a kowanne zabe.

Kara karanta wannan

An fallasa shirin shawo kan talaka da shinkafa da taliya a zaben gwamnan Ekiti

INEC ta shirya gudanar da zabrn gwamnan Ekiti
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Joash Amupitan, a ofishinsa da ke a Abuja. Hoto: @inecnigeria.
Source: Twitter

Yan takarar gwamnan Ekiti mafi shekaru

An ji cewa akwai yan takarar gwamnan shida masu shekaru tsakanin 61 zuwa 67 sun bayyana a matsayin manyan masu takara a zaɓen gwamnan Jihar Ekiti.

Rahoto ya ce an bayyana ɗan takarar Jam’iyyar LP, Farfesa Oyebanji Olajuyin, a matsayin mafi tsufa a cikin takarar yana da shekaru 67.

Waɗannan tsofaffin 'yan siyasa da suke takara suna da tarihin aiki da ya shafi ilimi, diflomasiyya, hidimar gwamnati, kasuwanci da siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.