Ba Ɗan Kwankwaso Tikitin Mataimakin Ɗan Takarar Gwamna a NDC Ya Bar Baya da Kura
- An zabi Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar NDC
- Nadin Mustapha ya haifar da muhawara mai zafi a Kano, inda masu suka suka zargi Kwankwasiyya da inganta siyasar gado maimakon fifita ƙwarewa
- Masu goyon baya sun kare zaɓin, suna cewa ya cancanci matsayin saboda gogewarsa a gwamnati, yayin da NDC ta ce an yi zaɓin ne bayan shawarwari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Babban ɗa ga Rabi'u Musa Kwankwaso ya zama dan takarar mataimakin gwamnan Kano a NDC.
Nadin Mustapha Rabiu Kwankwaso ya jawo ce-ce-ku-ce da ake ganin bai dace a mishi wannan ta yi a jam'iyyar ba.

Source: Facebook
Wannan na zuwa ne bayan ɗan takarar gwamna na jam’iyyar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana shi a matsayin abokin takararsa gabanin zaɓen 2027, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Zaben fitar da gwani: APC ta yi martani bayan tsohon sufeta janar ya fice daga cikinta
An zabi Mustapha mataimakin dan takarar gwamna
An bayyana sunan Mustapha ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na tafiyar Kwankwasiyya.
Gwarzo ya ce an zaɓe shi ne saboda ƙwarewarsa, biyayyarsa da kuma halayen jagoranci, ya bayyana cewa zaɓin ya kasance wata dabara ta ƙarfafa damar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.
Ya ce Mustapha ya nuna ƙwazo a hidimar jama'a kuma zai taimaka wajen cika manufofin jam’iyyar a Kano.
Sai dai matakin ya haifar da ra’ayoyi mabambanta, inda wasu suka zargi shugabannin Kwankwasiyya da ƙoƙarin kafa siyasar iyali.

Source: Facebook
Ja'afar Ja'afar ya soki zabin Mustapha Kwankwaso
Daga cikin masu suka akwai ɗan jarida Jaafar Jaafar, wanda ya bayyana a Facebook cewa nadin ya saɓa wa manufofin da aka kafa tafiyar Kwankwasiyya a kansu.
Ya ce mukamin mataimakin gwamna yana buƙatar gogewa, jimawa a siyasa da kuma ƙwarewar gudanarwa.
Jaafar ya ce duk da girmamawar da yake yi wa Sanata Kwankwaso, ya kamata a sake duba matakin.
Ya kuma yi zargin cewa Mustapha bai kai matsayin da zai iya jagorantar al'amuran miliyoyin mutane ba idan buƙatar hakan ta taso.
Sai dai wasu mambobin Kwankwasiyya sun kare Mustapha Kwankwaso, suna cewa mutane suna kallon sunansa ne kawai maimakon ayyukan da ya yi.
Jam’iyyar APC a Kano ta kuma yi amfani da batun wajen zargin Kwankwaso da ƙoƙarin ci gaba da rinjayar siyasar Kano ta hannun ɗansa.
NDC ta kare matakin sabon Mustapha Kwankwaso
Amma NDC ta yi watsi da zarge-zargen, tana mai cewa an yi zaɓin ne bayan gudanar da shawarwari kan lamarin.
Mai magana da yawun ɗan takarar gwamna, Ibrahim Shuaibu, ya ce shugabannin jam’iyyar na Kano ne suka fara gabatar da sunan Mustapha.
Ya ce bayan tattaunawa da nazari mai zurfi, Aminu Abdussalam Gwarzo ya amince da shi a matsayin abokin takara.
Kwankwaso ya magantu kan sabuwar dokar NDC
An ji cewa jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tofa albarkacin bakinsa kan sabuwar dokar da jam'iyyar NDC ta bullo da ita.
Dan takarar mataimakin shugaban kasar a zaben 2027 ya nuna cewa dokar abu ne wanda suka dade suna magana a kai.
Dokar dai mai neman hana 'yan siyasa sauya sheka bayan cin zabe ba ta shafi Peter Obi da madugun na Kwankwasiyya ba.
Asali: Legit.ng
