Yadda INEC Ta Yi Fatali da Maganar Takarar Jonathan a 2027

Yadda INEC Ta Yi Fatali da Maganar Takarar Jonathan a 2027

  • Hukumar INEC ta ce ba ta amince da takarar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da bangaren Kabiru Turaki na PDP ya ce ya mika mata ba
  • Bangaren Turaki ya ce ya mika sunayen Jonathan da sauran 'yan takararsa da hannu bayan INEC ta ki ba su lambobin shiga tsarin intanet
  • Rikicin shugabanci a PDP ya kara tsananta yayin da bangaren Turaki ke zargin INEC da nuna son kai kan rikicin cikin gida na jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi watsi da takarar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, da bangaren Kabiru Turaki na jam'iyyar PDP ya ce ya mika mata domin zaben shekarar 2027.

Bangaren Turaki ya dage cewa ya mika sunayen Jonathan da sauran 'yan takarar jam'iyyar da hannu ga INEC, lamarin da ya kara bayyana rikicin shugabanci da ke addabar PDP.

Kara karanta wannan

ADC ta bukaci Tinubu ya ceto daliban Borno kamar na Oyo

Shugaba Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa daraktar wayar da kan masu kada kuri'a da hulda da jama'a ta INEC, Victoria Eta-Messi, ta ce hukumar ba ta karbar sunayen 'yan takara ta kowace hanya face ta hanyar tsarin intanet da aka tanada.

Matsayar INEC kan takarar Jonathan

Victoria Eta-Messi ta bayyana cewa dokoki da ka'idojin hukumar sun tanadi cewa mika sunayen 'yan takara ta hanyar kafar intanet ake yinsa kadai.

Ta ce:

"Ana mika sunayen 'yan takara ne kawai ta hanyar tsarin da aka tanada kamar yadda dokoki da ka'idojinmu suka bayyana."

Sai dai sakataren yada labarai na bangaren Turaki, Kwamared Ini Ememobong, ya ce sun zabi mika sunayen da hannu ne bayan INEC ta ki ba su lambobin shiga da ake bukata domin amfani da tsarin intanet.

Bangaren Turaki ya zargi INEC

Ememobong ya ce duk da rashin ba su lambobin shiga, sun mika sunayen 'yan takarar jam'iyyar cikin cikakken bin dokar zabe ta 2026.

Kara karanta wannan

Dattawan Kiristoci sun yi matsaya kan tazarcen Tinubu a zaben 2027

Ya ce sunayen da suka mika sun hada da na Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa da kuma na 'yan takarar gwamnoni, majalisun dokoki na kasa da na jihohi.

Ya gargadi INEC da kada ta wallafa wani jerin sunayen da ya saba da wanda suka mika, yana mai cewa za su bi duk hanyoyin doka domin kare jam'iyyar.

Joasha Amupitan a ofishin INEC
Shugaban hukumar zabe ta kasa, Joasha Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Har ila yau, Ememobong ya ce rikicin ya samo asali ne bayan hukuncin Kotun Koli ya bar PDP ba tare da halastacciyar shugabanci ta kasa ba, lamarin da ya sa suka kafa kwamitin rikon kwarya tare da neman mafita a kotu.

Ya kuma zargi INEC da rashin nuna tsaka-tsaki wajen tafiyar da rikicin, yana mai cewa hakan ya kara tabbatar da zargin da ake yi cewa hukumar ba ta da cikakken adalci.

An nemi tura Jonathan UN

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar APRC ta bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsayar da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan takarar mukamin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya (UN).

Kungiyar ta ce Jonathan na da gogewar shugabanci, kwarewar diflomasiyya da kuma tarihin dimokuradiyya da suka dace da jagorantar babbar cibiyar ta duniya.

APRC ta kara da cewa gogewar Jonathan a matsayin mataimakin shugaban kasa da kuma shugaban Najeriya ta nuna yana da cikakken kwarewar gudanar da manyan al'amuran kasa da kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng