Tinubu Ya Sake ba da Muƙami a Gwamnatinsa, Ya Nada Ɗan Tsohon Gwamnan Plateau

Tinubu Ya Sake ba da Muƙami a Gwamnatinsa, Ya Nada Ɗan Tsohon Gwamnan Plateau

  • Shugaba Bola Tinubu ya sake naɗin wani mutum a matsayin hadiminsa na musamman a fadar shugaban kasa
  • Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya sanar da naɗin yayin bikin cika shekaru 80 da ƙaddamar da littafin tarihin Jonah Jang a Jos
  • Naɗin ya zo ne yayin da manyan shugabannin siyasa suka taru domin karrama Jonah Jang saboda gudummawar da ya bayar a aikin soja da siyasa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa ɗan tsohon gwamnan jihar Plateau mukami hadiminsa na musamman.

Tinubu ya Yakubu Jang, ɗan tsohon gwamnan Filato, Jonah Jang, a matsayin Babban Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ƙasa.

Tinubu ya ba dan tsohon gwamnan Plateau mukami a gwamnatinsa
Tsohon gwamnan jihar Plateau, Jonah Jang. Hoto: Yakubu Jang.
Source: Twitter

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da saƙon fatan alheri a madadin Shugaba Tinubu a bikin cika shekaru 80 da haihuwar Jonah Jang, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Malami ya bankado 'sirrin' Tinubu game da neman cin zabe ta kowace hanya

Tinubu ya nada dan tsohon gwamna mukami

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an sanar da wannan naɗi a ranar Asabar 1 ga watan Agustan shekarar 2026.

Shettima ya ce:

“A madadin Mai Girma Shugaban Ƙasa, ina farin cikin sanar da naɗin Yakubu Jang a matsayin Babban Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ƙasa.”

An sanar da wannan naɗi ne a babban bikin da aka gudanar a dakin taro na Tamarald da ke Jos, inda manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar suka halarta.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, gwamnoni, jami'an gwamnatin tarayya da jihohi, sarakunan gargajiya da sauran fitattun mutane.

Dan tsohon gwamna ya samu mukami a gwamnatin Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Jonah Jang. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Shettima ya yaba salon mulkin Tinubu

Shettima ya bayyana cewa naɗin ya nuna yadda Shugaba Tinubu ke yaba ƙwarewa, aminci da kuma muhimmancin bai wa mabambantan ra'ayoyi damar ba da gudummawa a shugabanci, cewar rahoton Tribune.

Baƙi da shugabannin siyasa da abokan hulɗar iyalan Jang sun yi maraba da sanarwar naɗin tare da tafa hannu, yayin da aka ci gaba da gudanar da bikin cikin annashuwa.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shugaban ƙaramar hukuma ya nada hadimi a bangaren rawa

A yayin bikin, Jonah Jang ya ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna Airman to Politics: My Life, wanda ke bayyana tafiyarsa daga aikin soja zuwa siyasa.

Mutane da dama musamman manyan ƴan siyasa da dama sun halarci bikin yayin da suke yabon Jang saboda gudummawar da ba al'umma a jihar da kasa baki daya.

Jonah Jang ya mulki jihar Plateau ne daga shekarar 2007 zuwa 2015 karkashin jam'iyyar PDP kafin Joshua Dariye ya gaji kujerar tasa.

Jang ya bukaci Mutfwang ya yi murabus

A baya, an ji cewa tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang ya nuna damuwa kan yadda yan siyasa ke sauya jam'iyya bayan sun samu mulki a Najeriya.

Jang ya bukaci Gwamna Caleb Mutfwang ya bar wa PDP kujerarsa saboda a inuwarta ya ci zabe a shekarar 2023 da ta gabata.

Ya kuma soki hukumar INEC bisa zargin katsalandan a harkokin jam'iyyun siyasa, yana mai cewa hakan barazana ce ga dimokuradiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.