Ana Tunkarar 2027, Atiku Abubakar Ya Aika Muhimmin Sako ga Matasan Najeriya
- Atiku Abubakar ya buƙaci matasan Najeriya su guji sayar da ƙuri'unsu, yana mai cewa hakan zai lalata makomarsu da hana samun shugabanci nagari
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce matasa su ƙi karɓar kuɗi, shinkafa ko wasu kyaututtuka domin zaɓen shugabannin da ba su cancanta ba
- Dan takarar ADC ya kuma buƙaci matasa su yi rajistar zaɓe, su kare ƙuri'unsu tare da gujewa rikicin siyasa da rarrabuwar kawuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya buƙaci matasan Najeriya da kada su sayar da ƙuri'unsu, yana mai gargadin cewa hakan zai hana su zaɓen shugabanni nagari tare da jefa makomarsu cikin haɗari.
Atiku ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin ƙaddamar da shugabannin jihohin ƙungiyar RUN, wata ƙungiyar matasa ta jam'iyyar ADC, a wani taron horas da shugabannin ƙungiyar da aka gudanar a Abuja.

Source: Getty Images
Atiku ya ce ƙuri'ar matasa ta fi kuɗi daraja
Da yake jawabi ga mahalarta taron, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce matasa su ne mafi rinjayen masu jefa ƙuri'a a Najeriya, don haka ya kamata su yi watsi da sayen ƙuri'u, rikicin siyasa da siyasar rarrabuwar kawuna.
Ya ce ƙuri'ar kowane ɗan ƙasa ta fi kowanne adadin kuɗin da ɗan siyasa zai iya bayarwa.
Atiku ya ce buhun shinkafa, kuɗi ko rigar yaƙin neman zaɓe duk za su ƙare, amma illar zaɓen shugabannin da ba su cancanta ba za ta ci gaba da shafar rayuwar al'umma na tsawon shekaru.
Ya ƙara da cewa sayar da ƙuri'a na nufin rasa damar samun ingantattun makarantu, asibitoci, ayyukan yi, wutar lantarki, tsaro da shugabanci na gari.
Ya buƙaci matasa su guji rikicin siyasa
Atiku ya kuma buƙaci matasa da kada su bari 'yan siyasa su yi amfani da su wajen tsoratar da abokan hamayya ko tayar da rikici a lokacin zaɓe.
Ya ce mafi alherin abin da matashi zai yi wa ɗan siyasa shi ne ya tabbatar cewa ya cancanci ƙuri'a ta hanyar nagarta, ƙwarewa, mutunci da kyawawan manufofi.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ƙalubalanci matasa da su mayar da tasirinsu a kafafen sada zumunta zuwa shiga siyasa a zahiri.
Ya buƙace su su yi rajistar zaɓe, su bayar da gudunmawa yayin gudanar da zaɓe, su yi aikin sa ido a rumfunan zaɓe tare da kare sahihancin zaɓe cikin lumana.
Atiku ya yi kira ga haɗin kan Najeriya
Atiku ya kuma roƙi matasa da su guji bambance-bambancen ƙabila da addini, yana mai cewa dukkan 'yan Najeriya suna fuskantar irin matsalolin tattalin arziki da zamantakewa.
Ya ce a zaɓen 2027 ya kamata a zaɓi shugabanni bisa cancanta, kyawawan ɗabi'u da ingantattun manufofi.
A ƙarshe, Atiku ya bayyana matasan Najeriya a matsayin babbar kadara ta ƙasa, yana mai ƙarfafa su su wayar da kan masu kaɗa ƙuri'a, taimaka wa masu jefa ƙuri'a karo na farko da kuma yin watsi da sayen ƙuri'u da tashin hankalin zaɓe.
Asali: Legit.ng

