Yana Shirin Barin Mulki, Gwamna a Arewa Ya Samu Rancen Dala Miliyan 91 daga ECOWAS

Yana Shirin Barin Mulki, Gwamna a Arewa Ya Samu Rancen Dala Miliyan 91 daga ECOWAS

  • Bankin EBID na ECOWAS ya amince da bai wa gwamnatin Bauchi rancen dala miliyan 91.63 domin gina tituna da gadoji 24 a faɗin jihar
  • Ana sa ran shirin zai samar da ayyukan yi 5,000 yayin aiwatar da shi, tare da ƙirƙirar guraben aiki 2,000 bayan kammalawa
  • Gwamna Bala Mohammed ya ce haɗin gwiwar zai bunƙasa tattalin arziki, inganta sufuri da ƙarfafa kasuwanci a tsakanin al'ummomin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi da Bankin Raya Tattalin Arziki da Zuba Jari na Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (EBID) sun rattaba hannu kan yarjejeniyar rancen dala miliyan 91.63 domin aiwatar da shirin inganta ababen more rayuwa na sufuri a jihar.

An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a hedkwatar bankin da ke Lomé, ƙasar Togo, tsakanin shugaban EBID, Dakta George Agyekum Donkor, da gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed.

Kara karanta wannan

Zargin almundahanar kudi: An fara shirin tsige kakakin majalisa a Najeriya

Gwamnatin Bauchi ta samu rancen $91.6 daga ECOWAS
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi yana gaisawa da shugaban bankin EBID na ECOWAS bayan samun rancen kudi. Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Bauchi ta samu rancen ECOWAS

Bisa yarjejeniyar, EBID zai samar da dala miliyan 91.63 domin gina da kuma kammala manyan ayyukan tituna da gadoji guda 24 a sassa daban-daban na jihar Bauchi, in ji rahoton Arise News.

Ana sa ran shirin zai inganta haɗin kai tsakanin birane da ƙauyuka, ya sauƙaƙa zirga-zirga zuwa kasuwanni da sauran muhimman ayyuka, tare da rage kuɗin sufuri.

Haka kuma, ana sa ran zai ƙarfafa harkokin noma da kasuwanci ta hanyar inganta hanyoyin jigilar kayayyaki a faɗin jihar.

Dubban matasa za su samu aiki

Shirin, wanda ya yi daidai da Tsarin Bunƙasa Jihar Bauchi da manufofin ci gaban Najeriya, ana sa ran zai samar da guraben aiki kusan 5,000 yayin aikin gini.

Bayan kammala ayyukan kuma, ana hasashen cewa mutane kusan 2,000 za su samu aikin yi na dindindin, lamarin da ake sa ran zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki cikin adalci.

Da yake jawabi a wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar, shugaban EBID, Dakta George Agyekum Donkor, ya ce bankin ya himmatu wajen tallafa wa manyan ayyukan raya ƙasa da ke samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Yadda aka kama mutum 2 da zargin cefanar da filayen gwamnatin Kano

Ya ce inganta hanyoyin sufuri a Bauchi zai rage kuɗin jigilar kayayyaki, ya sauƙaƙa isa kasuwanni, tare da buɗe ƙarin damar bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa da haɗin gwiwar yankin.

Gwamna Bala ya yabawa EBID

A nasa jawabin, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani babban ci gaba ga burin gwamnatin jihar na gina tattalin arziki mai ƙarfi da jure ƙalubale.

Ya ce ingantattun hanyoyin sufuri na taka muhimmiyar rawa wajen jawo masu zuba jari, bunƙasa kamfanoni masu zaman kansu da kuma inganta rayuwar al'umma.

ECOWAS ta ba Bauchi rancen kudin ne domin ayyukan titi da gadoji don inganta sufuri
Shugabannin kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS na gudanar da taro. Hoto: @ecowas_cedeao
Source: Facebook

Gwamnan ya gode wa EBID bisa wannan tallafi, yana mai cewa zai taimaka wa gwamnatin Bauchi wajen hanzarta aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa masu amfani ga tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

Bankin EBID ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa ya ƙara tabbatar da matsayinsa a matsayin muhimmin bankin raya ƙasashen Yammacin Afirka, wanda ke tallafa wa ƙasashe mambobi wajen aiwatar da manyan ayyukan ci gaba masu ɗorewa da tasiri.

ECOWAS: Za a fara aiki da sabon kudi

A wani labari, mun ruwaito cewa, Ƙungiyar ECOWAS ta sake tabbatar da aniyarta na ƙaddamar da kuɗin bai ɗaya na yankin Yammacin Afirka mai suna ECO a 2027.

Kara karanta wannan

Shiri ya kankama: Tinubu zai yi wani babban aiki na Naira tiriliyan 1.05 a Kano

Shugabannin ƙasashen ƙungiyar sun ce kuɗin zai ƙarfafa haɗin kan tattalin arziki da kasuwanci tsakanin ƙasashen yankin.

ECOWAS ta kuma nuna damuwa kan matsalar tsaro a yankin Sahel da kuma yawaitar garkuwa da mutane musamman a Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com