2027: Birtaniya za Ta Sa Ido kan Zaben Najeriya domin Tabbatar da Adalci

2027: Birtaniya za Ta Sa Ido kan Zaben Najeriya domin Tabbatar da Adalci

  • Birtaniya ta ce za ta cigaba da sa ido kan tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya kuma za ta ba da muhimmanci fiye da yadda aka saba ga babban zaɓen da ke tafe
  • Jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja yayin wata ziyarar da ya kai wa shugaban jam’iyyar APC
  • Dr Montgomery ya ce Birtaniya za ta ci gaba da mutunta ikon Najeriya a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, ya ce duk abin da ya faru a Najeriya ya shafe su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja a - Jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery, ya bayyana cewa za su tura masu sa ido domin bibiyar zaɓen gwamnonin da za a gudanar a jihohin Ekiti da Osun, a wani ɓangare na ƙoƙarin tabbatar da sahihancin tsarin zaɓe.

Kara karanta wannan

Wasu ƴan siyasa na daf da rasa tikitinsu, INEC ta yi watsi da wasu zaben fitar da gwani

Ya bayar da wannan tabbacin ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja.

Dr Richard Montgomery
Jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery. Hoto: @RMontgomeryUK
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa shugabannin biyu sun tattauna kan tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya, muhimmancin gudanar da zaɓe cikin lumana da sauransu.

Birtaniya za ta sa ido a zaben Najeriya

Yayin da ya ke magana kan zaben da za a gudanar a wasu jihohin Najeriya, Tribune ta rahoto Dr Montgomery ya ce:

“Za mu tura tawagogi domin sanya ido kan zaɓukan saboda waɗannan ne zaɓukan gwamna na ƙarshe da za a yi a wajen kakar babban zaɓe kafin babban zaɓen shekara mai zuwa.
"Muna son ganin an gudanar da zaɓe cikin lumana, sahihanci da nasara.”

Ya jaddada cewa Birtaniya na ci gaba da mutunta ikon Najeriya a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, tare da nuna matuƙar sha’awa kan ci gaban dimokuraɗiyya da tattalin arzikin ƙasar.

Martanin shugaban jam'iyyar APC

Yayin da yake maraba da babban jami’in diflomasiyyar, Farfesa Yilwatda ya bayyana Najeriya a matsayin ƙasar da zaman lafiyarta ke da matuƙar muhimmanci ba ga Afirka kaɗai ba har ma ga duniya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Bayan sukar kalamansa a 2023, Peter Obi ya shawarci matasa kan siyasar addini, kabilanci

“Mun yi maraba da zuwanku zuwa sakatariyar jam’iyyarmu. Najeriya ƙasa ce mai muhimmanci ba ga Afirka kaɗai ba har ma ga duniya gaba ɗaya. Zaman lafiyar Najeriya yana da muhimmanci ga Afirka da Turai.
"Rashin zaman lafiya a nan zai yi tasiri mai nisa a sassan nahiyar.
"Saboda haka dole ne mu yi aiki tare domin tallafa wa zaman lafiya da ci gaban ƙasarmu,”

In ji shi.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa
Shugaban APC, Nentawe Yilwatda a wajen taro. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

APC ta karbi mutanen Atiku Abubakar

A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar APC ta sanar da cewa ta karbi wasu magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ke ADC.

Kungiyar magoya bayan Atiku Abubakar da ta koma APC ta bayyana cewa ta dauki matakin ne saboda yadda Bola Tinubu ke kawo cigaba a Najeriya.

Yayin bikin karɓar kungiyar zuwa APC, shugabannin tafiyar sun tabbatar wa APC cewa za su samawa Bola Tinubu kuri'u miliyan 10 a zaben shugaban kasa na 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng