An Jikkata Yan Bindiga, an Hallaka da Dama, Wasu Sun Tsere da Munanan Raunuka
- Jami’an ‘yan sanda tare da sojoji da masu sa-kai sun tabbatar da cewa sun fatattaki wasu ƴan bindiga da dama
- Rahotannin sirri sun sa jami’an tsaro suka kai samame, amma ‘yan bindigar sun yi kwanton bauna kafin jami’an su mayar da martani da ƙarfi
- Kwamishinan ‘yan sandan Zamfara ya yaba da jajircewar jami’an tare da tabbatar da ci gaba da farmakin kawar da ‘yan bindiga domin kare rayuka da dukiyoyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Rahotanni sun tabbatar da wasu ƴan bindiga a jihar Zamfara sun kwashi kashinsu a hannun jami'an tsaro.
Jami’an rundunar ‘yan sandan Zamfara tare da sojoji da masu sa-kai sun dakile harin wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a hanyar Gidan Giye zuwa Magazu da ke ƙaramar hukumar Tsafe.

Source: Twitter
Jami'an tsaro sun jikkata yan bindiga a Zamfara
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:30 na ranar Juma’a bayan jami’an tsaro sun samu sahihan bayanan sirri cewa wasu manyan gungun ‘yan bindiga na ƙoƙarin tsallaka hanyar domin kai hari, cewar The Nation.
Da isarsu wurin, jami’an tsaron sun ci karo da ‘yan bindigar, amma nan take aka yi musu kwanton bauna yayin da maharan suka buɗe musu wuta mai ƙarfi.
Sai dai jami’an tsaron sun mayar da martani da ƙarfin wuta fiye da na maharan, lamarin da ya haddasa musayar wuta mai zafi har ‘yan bindigar suka tsere zuwa cikin daji.

Source: Original
Kokarin da ƴan sanda suka yi a Zamfara
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa an kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar yayin artabun, yayin da wasu da dama suka tsere ɗauke da raunukan harbin bindiga.
Ta kuma ce wata motar aikin rundunar ta CSK ta samu lalacewar tayoyi a lokacin artabun, amma hakan bai hana jami’an ci gaba da farmakin ba har sai da maharan suka janye.
Kwamishinan ‘yan sandan Zamfara, A.M. Bello, ya yaba da jarumtaka, ƙwarewa da jajircewar jami’an tsaron wajen fuskantar miyagun laifuffuka ba tare da ja da baya ba, cewar Daily Post.
Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙarfafa farmaki kan ‘yan bindiga da sauran masu aikata manyan laifuffuka domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Zamfara tare da dawo da zaman lafiya.
Zamfara na daga cikin jihohin da suke fama da hare-haren ƴan bindiga wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
Jami'an tsaro sun gwabza da ƴan bindiga
An ji cewa dakarun Operation Fansan Yamma sun yi artabu da mayaƙan Ado Allero inda aka dauki tsawon lokaci ana dauki ba dade a jihar Zamfara.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an dauki lokaci ana musayar wuta, lamarin da ya jawo mutuwar wasu da yawa yayin da wasu su ka samu raunuka.
Sojoji su na ci gaba da akin farautar fitinannun yan ta'addan da su ka addabi jama'a yayin da ake dakon wasu muhimman bayanai daga rundunar sojin kasa.
Asali: Legit.ng

