Siyasar Gombe Ta Ɗauki Zafi, Dan Takarar Gwamna Ya Kai Korafi ga Ƴan Sanda

Siyasar Gombe Ta Ɗauki Zafi, Dan Takarar Gwamna Ya Kai Korafi ga Ƴan Sanda

  • Dan takarar gwamnan APC a Gombe, Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, ya kai korafi ga Sufeto Janar na 'yan sanda kan zargin bata suna
  • Gwamna ya bukaci cibiyar yaki da laifukan intanet ta 'yan sanda tare da hadin gwiwar INTERPOL su binciko masu yada rahoton karya cewa EFCC ta kama shi
  • Magoya bayansa sun ce masu adawa sun koma yada karya domin dakile karbuwarsa, yayin da har yanzu 'yan sanda da EFCC ba su fitar da wata sanarwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Pantami, Gombe - Dan takarar gwamnan jam'iyyar APC a Gombe, Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, ya mika takardar koke ga Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya.

Jamilu Gwamna ya kai mika takardar koke ne kan zargin cin zarafi ta intanet, bata suna da kuma yada labaran karya gabanin zaben 2027.

Kara karanta wannan

ADC ta bukaci Tinubu ya ceto daliban Borno kamar na Oyo

Jamilu Gwamna ya yi korafi kan zargin bata suna
Dan takarar gwamnan APC a Gombe, Jamilu Isiyaku Gwamna. Hoto: Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna.
Source: Facebook

EFCC: Bukatar Jamilu kan zargin cin mutuncinsa

Majiyoyi da suka san abin da ke cikin koken sun ce Gwamna ya bukaci Cibiyar Yaki da Laifukan Intanet ta Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta fara bincike cikin gaggawa tare da hadin gwiwar INTERPOL, cewar The Nation.

An ce ya nemi hadin kan INTERPOL ne bayan wasu bayanan sirri sun nuna cewa wasu daga cikin wadanda ake zargin suna gudanar da wannan kamfen na intanet suna aiki ne daga wajen Najeriya.

Rahotanni sun ce koken ya ambaci wasu shafukan sada zumunta da ake zargi da yada ikirarin karya cewa Hukumar EFCC ta kama tare da tsare Dakta Gwamna.

Sai dai Gwamna ya musanta wannan zargi baki daya, yana mai cewa babu gaskiya a cikin rahotannin da aka wallafa game da kama shi ko tsare shi.

Abin da ya fusata Jamilu Gwamna a Gombe

A cikin takardar koken, an bayyana cewa wallafe-wallafen wani shiri ne na yada bayanan bogi domin rikitar da jama'a, bata masa suna da kuma karkatar da ra'ayin masu zabe.

Kara karanta wannan

Dattawan Kiristoci sun yi matsaya kan tazarcen Tinubu a zaben 2027

Ya bukaci 'yan sanda su nemi bayanan masu amfani da shafukan, adireshin IP da sauran hujjojin daga kamfanin Meta, su gano masu daukar nauyin wannan aiki tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Magoya bayan Gwamna sun bayyana cewa sun yi imanin binciken zai tona asirin masu wannan kamfen na bata suna, yayin da suka ce masu kada kuri'a za su zabi nagarta, kwarewa da hangen nesa.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar 'yan sanda da EFCC ba su ce komai kan koken ba wanda dan takarar ya mika.

Ƙarin bayani na tafe ...

Pantami ya bukaci a yi tonon silili

A baya, kin ji cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana dalilinsa na shiga takarar gwamnan Gombe a 2027, yana mai korafi kan lalacewar lamura.

Pantami ya bayyana cewa babu wata al'umma da ta gyaru da kanta, yana mai cewa sai mutane sun tashi tsaye domin neman sauyi.

Tsohon ministan ya bukaci a shirya muhawara tsakanin dukkan 'yan takara, tare da binciken ayyukansu da ba da damar tonon silili kafin zaben gwamna na 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.