Sababbin Bayanai Sun Fito kan Zargin Tsohon Gwamna game da Juyin Mulkin Tinubu
- Ana ci gaba da sake samun sababbin bayanai game da zargin tsohon gwamna da ake zargi da hannu a juyin mulki
- Takardun bincike sun nuna Kanar Mohammed Ma’aji ya ce tsohon gwamnan ya fara ƙin shiga shirin, amma daga baya ya canja ra'ayi bayan tattaunawa
- Tsohon gwamnan ya musanta zargin hannu a shirin juyin mulki, yana mai cewa shi mai bin tsarin dimokuraɗiyya ne da shugaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sababbin bayanan binciken sun gano yadda ake zargin tsohon gwamna ya fallasa wasu abubuwa kan yunkurin juyin mulki.
An ce tsohon ministan albarkatun mai, Timipre Sylva, ya shiga cikin shirin juyin mulkin da aka ce an yi ƙoƙarin yi wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2025.

Source: Facebook
Juyin mulki: Yadda aka binciko bayanansu
Rahoton Premium Times ya ce masu bincike sun tattara takardu sama da shafuka 7,400 da suka haɗa da bayanan waɗanda ake zargi.
Majiyoyi suka cedaga cikin bayanan akwai taunawarsu a ɓoye da sauran hujjojin da ake amfani da su wajen gurfanar da waɗanda ake zargi da hannu a shirin.
An ce mutane da dama, ciki har da jami'an soja masu aiki da masu ritaya da wasu fararen hula, na fuskantar shari'a a Kotun Soja da kuma Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Ko da yake har yanzu ba a kama Timipre Sylva ko gurfanar da shi a matsayin wanda ake tuhuma ba, rahoton ya ce sunansa ya fito cikin tuhume-tuhumen, yayin da ake zargin wasu tsoffaffin hadimansa sun ɓoye bayanai kan inda yake.

Source: Facebook
Juyin mulki: Rawar da tsohon gwamna ya taka
Rahoton ya ce masu bincike sun yi zargin cewa Sylva ne ya bayar da mafi yawan kuɗin da aka tara domin shirin juyin mulki, inda aka ce ya aika kusan naira miliyan 785 ta wani kamfani zuwa hannun masu musayar kuɗi kafin kuɗin ya isa ga waɗanda aka nufa.
A cikin bayanansa ga masu bincike, Kanar Mohammed Ma’aji ya ce ya daɗe yana sanin Sylva tun yana kyaftin a rundunar soji, kuma daga baya ya nemi taimakonsa saboda ƙungiyar na fama da ƙarancin kuɗaɗe.
Ma’aji ya ce da farko Sylva ya ƙi shiga shirin tare da cewa ba ya son a haɗa shi da harkokin soja, sai dai daga baya ya sake kiran sa domin jin cikakken bayani da kuma yiwuwar nasarar shirin.
Rahoton ya ce Ma’aji ya yi zargin cewa Sylva ya amince da ba da kuɗi, amma ya nemi a bi hanyar da ba za ta nuna alaƙarsa da kuɗin ba.
Sai dai Sylva ya musanta dukkan zarge-zargen, yana mai bayyana kansa a matsayin mai bin tafarkin dimokuraɗiyya kuma mai goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.
Yadda aka shirya afkawa fadar Aso Rock
An ji cewa an fahimci yadda sojoji suka yi tsare-tsare na musamman da nufin hambarar da Bola Tinubu daga kan karaga.
Bayanai sun nuna yadda ake shirin mamaye Fadar Shugaban Ƙasa da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama.
Sojojin da ake zargi da shirin tawaye sun rika amfani da kalmomin "noma" da "girbi" don boye shirin juyin mulkin.
Asali: Legit.ng

