Hisbah Ta Dawo kan Masu Adaidaita Sahu, Ta Kakaba Doka game da Daukar Mata

Hisbah Ta Dawo kan Masu Adaidaita Sahu, Ta Kakaba Doka game da Daukar Mata

  • Hukumar Hisbah ta Kano ta haramta tsarin daukar mata da direbobin adaidaita sahu ke tana mai cewa ya saɓa wa koyarwar Musulunci
  • Hisbah ta sanar da umarnin ne yayin ganawa da shugabannin BOTORA, inda suka tattauna hanyoyin inganta tsari
  • Ta kuma buƙaci haɗin kai wajen yaƙi da satar yara, fataucin miyagun ƙwayoyi da rashin ɗa’a, yayin da BOTORA ta yi alƙawarin bin umarnin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Hukumar Hisbah ta Kano ta sake kawo sabuwae doka kan ayyukan masu adaidaita sahu domin tsabtace ayyukansu.

Hukumar ta haramta tsarin da ake kira “attachment”, inda direbobin adaidaita sahu ke ɗaukar mata a gefen babur ɗin adaidaita sahu.

Hisbah ta kawo doka a ayyukan masu adaidaita sahu
Shugaban hukumar Hisbah a Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa. Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Source: Facebook

Mataimakin kwamishinan Hukumar Shari’ar Kano, Sheikh Ali Danabba, ne ya sanar da wannan mataki yayin wata ganawa da shugabannin ƙungiyar masu adaidaita sahu ta BOTORA, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shugaban ƙaramar hukuma ya nada hadimi a bangaren rawa

Adaidaita sahu: Hisbah ta hana daukar mata

Hukumar ta ce wannan ya saɓa wa koyarwar addinin Musulunci saboda kusancin jiki tsakanin direba da fasinja mace.

An shirya taron ne domin ƙarfafa haɗin kai wajen inganta tsari da ƙwarewa a harkar sufuri.

Danabba ya bayyana cewa dole ne direbobi su daina ɗaukar mata a gefen adaidaita sahu ta hanyar tsarin “attachment” nan take.

Ya ce tsarin ya haramta a Musulunci saboda yana haifar da kusancin jiki da ba dole ba tsakanin namiji da mace.

Ya ce an gudanar da taron ne domin ƙara haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Shari’a da ƙungiyar BOTORA wajen magance matsalolin da ke shafar Kano da kuma inganta zaman lafiya.

A yayin taron, an kuma tattauna hanyoyin da za a bi wajen yaƙi da satar yara, daƙile amfani da fataucin miyagun ƙwayoyi, tare da ƙarfafa ɗa’a da kyawawan halaye a tsakanin direbobin adaidaita sahu.

Kara karanta wannan

'Ku dakatar da gina gadar sama': Tinubu ga gwamnoni, ya kawo masu mafita

Hisbah ta hana daukar mata a gefen direban adaidaita sahu
Jami'an hukumar Hisbah yayin da suke sintiri a cikin birnin Kano. Hoto: AMINU ABUBAKAR/AFP via Getty Images.
Source: Twitter

Bukatar Hisbah game da sabuwar dokar

Sheikh Danabba ya buƙaci dukkan masu adaidaita sahu su bi sabon umarnin tare da ba da haɗin kai domin bunƙasa kyawawan ɗabi’u, tabbatar da doka da oda da kuma kare lafiyar al’umma a Kano.

Da yake jawabi, shugaban BOTORA ya tabbatar da cewa ƙungiyarsa za ta yi cikakken haɗin gwiwa da Hukumar a Kano wajen tabbatar da tsaro, zaman lafiya da ci gaban jihar, cewar Punch.

Taron ya samu halartar Mataimakin Kwamishinan Hukumar Shari’ar Kano Sheikh Ali Danabba, Kwamishina Gwani Dahir Yakasai, daraktoci da sauran manyan jami’an hukumar, tare da shugaban BOTORA da mambobin kwamitinsa.

Hisbah ta kawo dokoki kan aure a Sokoto

An ji cewa Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto ta sanar da haramta wasu al'adu da ake yi a bukukuwa da shagulgulan aure.

Daga cikin abubuwan da aka haramta akwai "Na Gani In So", kidan DJ, Wazigidi da wasu dabi'un da hukumar ta ce sun saba wa koyarwar Musulunci.

Hukumar ta gargadi masu shirya bukukuwa da iyalai su bi umarnin, tana mai cewa za ta dauki mataki kan masu karya dokar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.