An Kuma Dage Shari'ar Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufai

An Kuma Dage Shari'ar Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufai

  • Babbar Kotun Tarayya da ke zama a gain Kaduna ta dage sauraron karar tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai
  • Hukumar yaki da rashawa ta ICPC na tuhumar tsohon gwamnan da laifuffukan cin amanar ofis da almundahana lokacin mulkinsa
  • Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro sun kawo El-Rufai gaban kotu a zaman na yau Litinin, amma sauran wadanda ake tuhuma ba su halarta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna ta dage ci gaba da sauraron shari’ar tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufai, zuwa ranar 28 ga Yuni, 2026.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ce ta shigar da karar, inda take zargin El-Rufai da laifuffukan cin amanar ofis, zamba da kuma wasu matsalolin da suka shafi yadda aka gudanar da harkokin kudi a lokacin mulkinsa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun lalata shirin kai harin bama bamai kan matafiya a jihar Zamfara

El Rufai.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Facebook

Jami'an tsafo sun kawo Nasir El-Rufai kotu

Tashar Channels tv ta ce a zaman kotun na ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, 2026 an kawo El-Rufai kotun da misalin karfe 9:30 na safe tare da rakiyar jami’an ICPC, DSS da kuma ’yan sanda.

Tun a baya, zaman kotun ya fi mayar da hankali ne kan bukatar belin da tsohon gwamnan ya gabatar da kuma muhawarar shari’a da ta biyo baya.

Masu gabatar da kara sun yi zargin cewa an fitar da kudade domin gudanar da wasu ayyuka da ba a aiwatar ba ko kuma aka gudanar da su ba bisa ka’ida ba a mulkin El-Rufai.

Kara karanta wannan

Bincike: 'Yan bindiga ne suka mika gawar Janar Rabe hannu da hannu? Gaskiya ta fito

Sai dai El-Rufai ya ci gaba da jaddada cewa ba shi da laifi a duka tuhume-tuhumen da ake masa, yana mai cewa bai aikata wani laifi ba.

Rikicin kan batun belin El-Rufai

A ranar 14 ga Afrilu, 2026, Mai Shari’a Rilwan Aikawa ya amince da bayar da belin El-Rufai kan kudi Naira miliyan 200.

Daga cikin sharuddan belin akwai samar da mutane biyu da za su tsaya masa kuma daya daga cikinsu ya kasance ma’aikacin gwamnati ko wanda ya yi ritaya daga matakin GL 15 ko sama da haka.

Yayin da lauyoyin El-Rufai suka nemi a sassauta sharuddan belin a Babbar Kotun Tarayya, wata Babbar Kotun Jihar Kaduna karkashin Mai Shari’a Darius Khobo ta ki amincewa da bukatar bayar da beli a wani bangaren karar.

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a zaman kotu a Najeriya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Dalilin dage shari’ar a wannan karo

Rahoton Vanguard ya nuna cewa an shirya ci gaba da sauraron bukatu da hujjojin bangaren masu kara da masu kare kai a zaman na yau Litinin.

Kara karanta wannan

Rana ta 3: Masu zanga zanga sun toshe titi mai muhimmanci a Abuja kan matsalar tsaro

Sai dai kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 28 ga Yuni, 2026, saboda rashin halartar wasu daga cikin wadanda ake tuhuma tare da El-Rufai a karar.

ICPC ta hana ganin Malam El-Fufai

A wani labarin, kun ji cewa ADC ta zargi ICPC da hana shugabanninta ganawa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, a hedikwatar hukumar Abuja.

ADC ta ce yadda aka jibge jami’an tsaro a wajen hedikwatar hukumar ICPC ya nuna ana amfani da hukumomi wajen tsoratar da ‘yan adawa.

Tawagar da ta kai ziyara ga El-Rufai ta kunshi sakataren jam’iyyar na kasa, Ogbeni Rauf Aregbesola; sakataren yada labarai, Bolaji Abdullahi da wasu jiga-jigi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262