Ana Tunkarar Zabukan 2027, Shugaban INEC Ya Dauki Sabon Alkawari ga Ƴan Najeriya

Ana Tunkarar Zabukan 2027, Shugaban INEC Ya Dauki Sabon Alkawari ga Ƴan Najeriya

  • Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ya ce kuri’un masu zabe za su yi tasiri a zaben gwamnan jihar Ekiti
  • Farfesa Josh Amupitan ya ce yawan masu rajistar zabe a jihar ya haura miliyan daya yayin da zaben zai gudana a watan gobe
  • Hukumar ta gargadi jam’iyyu da masu zabe kan sayen kuri’u yayin da Amupitan ya bada tabbacin INEC za ta yi adalci a zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ekiti - Shugaban hukumar INEC, Farfesa Josh Amupitan, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kuri’un da za a kada ne kawai za su yi tasiri a zaben gwamnan Ekiti.

Farfesa Amupitan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar tantance shirye-shiryen zabe da ya kai jihar Ekiti tare da sauran kwamishinonin INEC kafin zaben gwamna da za a gudanar ranar 20 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke bayan zaben fitar da gwanin APC, an kashe mutum 1 a jihar Kaduna

Shugaban INEC ya sha alwashin gudanar da sahihin zabe a jihar Ekiti.
Shugaban INEC, Farfesa Josh Amupitan (tsakiya) yana jawabi a ofishin hukumar da ke Abuja. Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

Shugaban INEC ya ziyarci jihar Ekiti

A yayin taron, shugaban INEC ya kuma gabatar da kundin rajistar masu kada kuri’a ga jam’iyyun siyasa kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Shugaban INEC ya bayyana muhimmancin rajistar masu kada kuri’a wajen tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe

Amupitan ya bayyana taron a matsayin wani abu mai matukar muhimmanci ga hukumar, yana mai cewa ba kasafai ake samun jihar da za ta karbi bakuncin shugaban INEC tare da kusan dukkan kwamishinonin kasa ba.

Ya ce dokar zabe ta tanadi cewa dole ne a wallafa tare da gabatar da kundin masu kada kuri’a ga jam’iyyun siyasa kwanaki 30 kafin gudanar da zabe.

A cewarsa, cikin manyan ayyuka tara da hukumar ta tsara domin zaben, an kammala guda bakwai, yayin da za a kammala yakin neman zabe ranar 18 ga watan Yuni.

Yawan masu rajistar zabe a jihar Ekiti ya karu

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya hakura da takara, ya janye daga zaben fitar da gwanin APC

Farfesa Amupitan ya bayyana cewa an samar da kundin masu kada kuri’a ne bayan tattara bayanai da tantancewa mai zurfi domin tabbatar da sahihancinsa.

Ya ce yawan masu rajistar zabe a jihar Ekiti ya karu sosai bayan gudanar da rajistar katin zabe ta dindindin watau CVR, in ji rahoton Vanguard.

A cewarsa, daga kusan masu zabe 900,000 da jihar ke da su a baya, yanzu adadin ya kai kimanin mutum 1,059,360.

Ya kara da cewa INEC ba za ta iya gudanar da sahihin zabe ita kadai ba, saboda hakan na bukatar hadin kan jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.

Shugaban hukumar INEC ya ziyarci jihar Ekiti gabanin zaben gwamna
Ana Tunkarar Zabukan 2027, Shugaban INEC Ya Dauki Sabon Alkawari ga Ƴan Najeriya
Source: Original

INEC ta aika sako ga jam’iyyun siyasa

Shugaban hukumar ya bukaci jam’iyyun siyasa su wayar da kan magoya bayansu domin fitowa su kada kuri’a a ranar zabe.

Ya sake jaddada cewa kuri’un jama’a za su yi tasiri, yana mai buga misali da yadda ake tura sakamakon zabe kai tsaye ta hanyar RVP a zabukan baya.

Amupitan ya kuma nuna damuwa kan matsalar sayen kuri’u, yana mai bayyana hakan a matsayin babban kalubale ga dimokuradiyyar Najeriya.

Kara karanta wannan

"Za su yi amfani"; Shugaban INEC ya ba masu kada kuri'a tabbaci kan zabe a Najeriya

Babu sunan PDP a rajistar zaben Ekiti

A wani labari, mun ruwaito cewa, INEC da jam'iyyun siyasa na ci gaba da shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Ekiti, wanda za a gudanar a watan Yunin 2026.

Rahoto ya tabbatar da cewa INEC ta fitar da jerin sunayen 'yan takara 12 da mataimakansu, wadanda za su fafata a zaben gwamnan Ekiti.

Sai dai abin da ya ja hankali shi ne rashin ganin sunan dan takarar gwamnan PDP da mataimakinsa, wanda ake ganin yana da alaka da rikicin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com