'Yan Siyasan da Suka Ki Barin Jam'iyyar PDP har Yau duk da Rikicin Cikin Gida
Abuja - Duk rigimar da ya dabaibaye jam’iyyar adawa ta PDP, akwai wasu ‘yan siyasa da har yanzu suna nan ba su canza gida ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
A yanzu da ake watan Yulin 2026, Legit Hausa ta yi kokarin duba manyan ‘yan siyasar da har gobe suna nan a cikin jam’iyyar PDP.
Rigimar PDP tsakanin bangaren yaran Nyesom Wike da Kabiru Tanimu Turaki ya kai intaha.

Source: Getty Images
‘Yan siyasar da suka ki barin jam’iyyar PDP
1. Nyesom Wike
Rigimar cikin gidan da ya addabi PDP bai sa Nyesom Wike ya sauya-sheka ba duk da ya samu mukamin minista a gwamnatin APC.
Tsohon gwamnan ya zabi ya cigaba da zamansa a PDP har yau, sai dai wasu na zargin yana da hannu a rikicin da aka shiga tun 2022.
Wasu ‘ya ‘yansa a siyasa sun raba kafa, ana iya ganin mutanensa da yanzu suna cikin APC amma shi ya cigaba da zama da rajistar PDP.

Kara karanta wannan
An ji labarin abin da aka tattauna da Peter Obi ya zauna da Jakadan kasar Switzerland
2. Natasha Akpoti-Uduaghan
Wannan rigimar da ake yi a PDP duk bai damu Natasha Akpoti-Uduaghan ba. Sanatar Kogi ta tsakiya tana cikin wadanda ba su canza sheka ba.
Rigimar cikin gida ya jawo PDP ta rasa sanatoci da-dama a Majalisar dattawa, amma 'yar siyasar ta zabi kasancewa a jam’iyyar da ta taimake ta.
Akwai yiwuwar Natasha Akpoti-Uduaghan za ta kara da jam’iyyar ADC da tsohon gwamnan Kogi a zaben 2027 wajen neman tazarce.
3. Ibrahim H. Dankwambo
Shi ma Ibrahim Hassan Dankwambo OON bai rabu da PDP har zuwa yanzu. Sanatan na Arewacin Gombe ya ki yin sallama da jam’iyyar.
Sanatan bai batulcewa jam’iyyar da ta ba shi damar zama gwamna na shekaru takwas a jihar Gombe ba, bayan nan ta kai shi Majalisar dattawa.
Masu nazarin siyasa na ganin tasirinsa za su taimaki PDP a zaben gwamnan jihar Gombe.
4. Sule Lamido
A sa’ilin da wasu suke yin bakin kokarinsu na rabuwa da PDP, lokacin Sule Lamido yake neman yadda zai zama shugaban jam’iyya na kasa.
Tsohon gwamnan Jigawa yana cikin masu kishin PDP kuma an saba ji yana maida martani ga wadanda suka taba masu jam’iyya.
Alhaji Sule ya rike mukamin minista da gwamna a shekaru 16 da jam’iyyar ta yi a ofis.
5. Ahmad Muhammad Karfi
Ahmad Muhammad Makarfi bai taba gigin shiga jam’iyya mai mulki ba, har yanzu tsohon gwamnan na Kaduna bai jefar da PDP ba.
Tsohon sanata na Kaduna ta Arewa ya rike shugabancin jam’iyyar PDP a mawuyacin lokaci kuma ya yi ta kokari wajen dinke baraka.
Ana ganin Makarfi bai dauki bangare a rigimar da ake yi ba, ya bukaci a bar doka ta yi aiki.

Source: Getty Images
6. Abubakar Bukola Saraki
Idan ana jero ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP, dole a hada da Abubakar Bukola Saraki. Babban ‘dan siyasar bai canza sheka ba tun 2018.
Daga lokacin da ya zabi ya rabu da jam’iyyar APC ya sake dawo wa PDP har yanzu tsohon shugaban majalisar dattawan bai yi rawa ba.
Saraki ya jagoranci kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP, sai dai wannan bai hana shi rasa abokan aikinsa zuwa sauran jam’iyyu ba.
Sauran wadanda suka ki barin PDP
Wasu shahararrun ‘yan siyasar da suka zabi cigaba da zama a PDP su ne Ambasada Umar Damagum da Sanata Sam Anyanwu.
Tsohon shugaban jam’iyyar bai sauya sheka ba, haka zalika Anyanwu yana tare da tsagin Nyesom Wike na jam’iyyar ta PDP har zuwa yau.
Masu neman takara a PDP sun shiga uku
INEC ta sa takarar ‘yan siyasa fiye da 2, 000 ta bi ruwa a jam’iyyar PDP da LP kamar yadda muka rahoto game da shirye-shiryen zaben 2027.
Fam din wasu masu neman takarar gwamna da majalisa na neman zama daidai da takardar tsire domin ba a iya daura sunayensu a shafin INEC ba.
Rikicin cikin gida da ya jawo bangaroroi a jam'iyyun na PDP da LP shi ne ya jawo wannan.
Asali: Legit.ng

