NDC: Mai Neman Takarar Sanata Ya Maka INEC da Jam'iyyarsu Kwankwaso a Kotu
- Isaac Nwachukwu ya kai ƙarar NDC da INEC kotu, yana neman a amince da shi a matsayin ɗan takarar sanata na Imo ta Arewa
- Mai neman takarar ya yi ikirarin cewa ya biya N25m ga NDC domin sayen fom da kuma tallafi ga jam’iyyar, amma daga baya aka cire sunansa
- Nwachukwu ya yi zargin cewa an sauya sunansa da na wani ɗan takara na daban duk da cewa an riga an amince da shi kuma an karbi kudinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Imo – Wani mai neman tikitin Sanata a mazabar Imo ta Arewa a ƙarƙashin NDC, Isaac Nwachukwu, ya kai ƙarar jam’iyyar da hukumar INEC a gaban babbar kotun tarayya da ke Owerri.
Nwachukwu na neman kotun ta tabbatar da shi a matsayin halastaccen ɗan takarar sanata na jam’iyyar domin shiga zaɓen shekarar 2027.

Source: Facebook
Nwachukwu ya maka NDC da INEC a kotu
A cikin ƙarar da ya shigar, Nwachukwu ya yi zargin cewa an hana shi tikitin jam’iyyar duk da cewa ya cika dukkan sharuɗɗan da aka gindaya masa, in ji rahoton Punch.
Ya ce bayan ya samu amincewar sauran masu neman takarar a matakin sulhu na tsayar da ɗan takara, daga baya aka cire sunansa tare da maye gurbinsa da wani mutum.
Isaac Nwachukwu ya bayyana cewa ya biya Naira miliyan 25 ga jam’iyyar domin neman tikitin takarar.
A cewarsa, Naira miliyan 20 daga cikin kuɗin tallafi ne ga jam’iyyar, yayin da Naira miliyan 5 kuma kuɗin sayen fom ɗin takara ne na kujerar sanatan Imo ta Arewa.
Abubuwan da yake nema a gaban kotu
Ya kuma ce ya halarci tantancewar da jam’iyyar ta shirya kuma an amince da shi a matsayin wanda ya cancanci shiga zaɓen fidda gwani.
Nwachukwu ya yi zargin cewa an samu kura-kurai a tsarin gudanar da zaɓen fitar da gwani, inda aka ware kuɗin da ya biya aka sanya sunan wani ɗan takara mai suna Matthew Omegara.
Daga cikin buƙatun da ya gabatar wa kotu akwai neman a ayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen ɗan takarar NDC na mazabar Imo ta Arewa.
Haka kuma yana son kotun ta hana jam’iyyar NDC tsayar da wani ɗan takara daban a zaɓen sanata na yankin, in ji rahoton Leadership.
Bugu da ƙari, ya nemi kotun ta umarci INEC da kada ta amince da takarar wani mutum a madadinsa har sai an kammala shari’ar.

Source: Getty Images
Ba a ji ta bakin INEC, NDC ba
A cikin takardar rantsuwar da ya gabatar, Nwachukwu ya ce bayan an amince da shi a matsayin ɗan takara na sulhu kuma aka saka sunansa cikin jerin waɗanda suka yi nasara, daga baya aka maye gurbinsa da wani ɗan takara ba tare da bin ƙa’idojin jam’iyyar da dokar zaɓe ba.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jam’iyyar NDC da INEC ba su fitar da wata sanarwa dangane da zarge-zargen da Nwachukwu ya yi a gaban kotu ba.
Martanin Kwankwaso kan dokar NDC
A wani labari, mun ruwaito cewa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tofa albarkacin bakinsa kan sabuwar dokar da jam'iyyar NDC ta bullo da ita.
'Dan takarar mataimakin shugaban kasar a zaben 2027 ya nuna cewa dokar abu ne wanda suka dade suna magana a kai.
Dokar dai mai neman hana 'yan siyasa sauya sheka bayan cin zabe ba ta shafi Peter Obi da madugun na Kwankwasiyya ba.
Asali: Legit.ng


