An Bankado Shirin Boko Haram na Sace 'Yan Siyasa, Sarakuna a Jihohin Arewa 2
- Hukumar DSS ta yi gargadin cewa ‘yan Boko Haram na shirin kai manyan hare-hare a ƙananan hukumomin Michika da Askira-Uba
- Rahoton ya ce ‘yan ta’addan na shirin yin garkuwa da manyan jami’an gwamnati, hakimai, fastoci da mazauna yankunan
- DSS ta buƙaci jami’an tsaro da masu gadin dazuka su ƙara tsaurara matakan tsaro domin hana hare-haren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Adamawa - Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta yi gargadin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram na shirin kai manyan hare-hare a jihohin Adamawa da Borno.
DSS ta yi gargadin cewa ana shirin kai hare-haren ne a ƙaramar hukumar Michika ta jihar Adamawa da kuma ƙaramar hukumar Askira-Uba ta jihar Borno.

Source: Original
A cewar wata takardar DSS da aka fallasa kuma TheCable ta gani, shirin kai hare-haren na da alaƙa da rushewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ‘yan ta’addan da gwamnatocin jihohin biyu.
Takardar ta ce ‘yan ta’addan na shirin yin garkuwa da manyan jami’an gwamnati, kansiloli, hakimai, fastoci da kuma mazauna yankunan da abin ya shafa.
Boko Haram ta shirya sace manyan jami’ai
“Bayanan sirri sun bayyana cewa ‘yan ta’addan Boko Haram na shirin gudanar da manyan hare-hare a ƙaramar hukumar Michika ta jihar Adamawa da kuma ƙaramar hukumar Askira-Uba ta jihar Borno domin nuna rushewar yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatocin jihohin suka yi,”
“‘Yan ta’addan na shirin yin garkuwa da manyan jami’an gwamnati, kansiloli, hakimai, fastoci da kuma mazauna ƙananan hukumomin."
“Bugu da ƙari, ‘yan ta’addan na shirin sace Hakimin Michika tare da ɗansa da ke zaune a gidansa.” In ji takardar.
DSS ta buƙaci a kara tsaro
Takardar ta ce ‘yan ta’addan sun riga sun tura wata tawagar leƙen asiri domin shirya kai harin.
DSS ta shawarci dakarun tsaro da masu gadin dazuka su ƙara ƙarfafa matakan tsaro a faɗin yankunan da abin ya shafa.

Kara karanta wannan
"Za mu auri kyayawan"; 'Yan bindiga sun yi sabuwar barazana kan mutane 176 da suka sace
Hukumar ta ce ƙara tsaurara tsaro zai taimaka wajen hana hare-haren da ake zargin ‘yan Boko Haram na shirin kaiwa.

Source: Facebook
Sojoji sun fara binciken kan fitar takardar
Rundunar sojojin Najeriya ta fara binciken yadda rahoton sirri na DSS da ke gargadin yiwuwar hare-haren ‘yan Boko Haram da wasu ‘yan bindiga a sassan jihohin Adamawa da Borno ya shiga hannun jama’a.
Binciken The Punch ya gano cewa manyan jami’an rundunar sojoji ta Bataliya ta 232 da ke Yola, jihar Adamawa, sun fara binciken cikin gida domin gano jami’in da ke da alhakin yaɗa takardar sirrin.
Batun alakar Ndume da Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ali Ndume, ya musanta zargin cewa ya taɓa karɓar kuɗin fansa ko zama mai shiga tsakani tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar Boko Haram.
Sanata Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce bai taɓa goyon bayan tattaunawa da Boko Haram ko biyan kuɗin fansa ba.
Asali: Legit.ng
