Sun Yi Laifi: Kotu Ta Ci Tarar Tsohon Gwamna da Jam'iyyar ADC Naira Miliyan 1

Sun Yi Laifi: Kotu Ta Ci Tarar Tsohon Gwamna da Jam'iyyar ADC Naira Miliyan 1

  • Wata kotun tarayya da ke Abuja ta ci tarar ADC da Rauf Aregbesola N1m bayan ta yi watsi da bukatar cire Mai shari’a Peter Lifu
  • Mai shari’a ya ce zargin cewa yana nuna son kai ba shi da tushe kuma yunƙuri ne na neman alkalin da zai yi wa masu karar biyayya
  • A yayin zaman, an kuma tafka muhara game da batun soke rajistar jam'iyyar ADC da yadda hakan zai iya shafar hukuncin yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatun da jam’iyyar ADC da sakatarenta na kasa, Rauf Aregbesola, suka gabatar gabanta.

Jam'iyyar ADC da sakatarenta na kasa, Rauf Aregbesola sun nemi alkalin kotun ya janye daga sauraron wata kara da ta shafi shugabancin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: An samu matsala a shari'ar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El Rufai

Kotu ta ci Aregbesola da ADC tarar N1m.
Ra'uf Aregbesola (tsakiya) a wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ADC a shiyyar Kudu maso Yamma a Ibadan. Hoto: @ADCNig
Source: Facebook

Kotu ta ci ADC da Aregbesola tarar N1m

Mai shari’a Peter Lifu ya bayyana cewa bukatun ba su da tushe balle makama, tare da umartar Aregbesola da ADC su biya takarar N500,000 kowanne, in ji rahoton Daily Trust.

Hakan ya kai jimillar tarar zuwa Naira miliyan daya da za a biya mai shigar da karar, kamar yadda rahoton ya nuna.

A hukuncinsa, Mai shari’a Lifu ya ce masu neman ya janye daga karar sun kasa gabatar da hujjoji masu karfi da za su tabbatar da zargin nuna son kai da suka yi masa.

Ya bayyana matakin a matsayin wata dabara ta neman sauya alkali domin a bai wa wani mai shari’a karar.

“Zargin nuna son kai babban zargi ne da ke bukatar kwararan hujjoji. Amma masu neman bukatar sun kasa tabbatar da zarginsu,” in ji Mai shari’a Lifu.

Ya kara da cewa kotu ba za ta bari masu kara ko wadanda ake kara su rika zabar alkalan da za su saurari kararrakinsu ba.

Kara karanta wannan

Trump ya ballo ruwa, 'yan majalisa sun bude masa wuta kan shirin yarjejeniya da Iran

Yadda rikicin ADC ya kai gaban kotu

Mai shari’ar ya ce idan aka amince da irin wannan bukata ba tare da hujja ba, hakan na iya zama wata hanya da lauyoyi za su rika amfani da ita wajen matsa lamba ga kotu.

Karar dai ta samo asali ne daga korafin wani dan jam’iyyar ADC mai suna Bala Nafiu, wanda ya kalubalanci sahihancin sabon tsarin shugabancin jam’iyyar.

Nafiu ya bukaci kotu ta hana David Mark, Rauf Aregbesola da sauran mambobin kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar ci gaba da bayyana kansu a matsayin shugabannin ADC.

Ya yi zargin cewa yadda aka nada su ya sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma dokar zabe.

Babbar kotun tarayya ta ce ADC da Aregbesola sun gaza gabatar da hujjojin cewa alkali ya nuna son kai.
Harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: Light Oriye Tamunotonye / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

An yi takaddama kan hukuncin soke rajistar ADC

A farkon zaman kotun, wani lauya mai suna Kalu-Kalu Agu ya yi kokarin hana kotun yanke hukunci kan bukatar janyewar mai shari’ar.

Ya yi nuni da cewa Mai shari’a Lifu ya riga ya yanke wani hukunci a ranar Litinin wanda ya umarci INEC ta soke rajistar ADC.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Peter Obi ya bayyana abin da zai fara yi game da Nnamdi Kanu

Sai dai lauyan Bala Nafiu, Robert Emukpoeruo (SAN), ya ce wannan batu ba shi da alaka da karar da ake saurare, in ji rahoton The Nation.

Mai shari’a Lifu ya amince da wannan hujja, yana mai cewa karar da ake saurare daban take da wadda ya yanke hukunci a kanta a baya.

Bayan kammala hukunci kan bukatar janyewar alkali, kotun ta dage ci gaba da sauraron dukkan bukatun da ke gabanta zuwa ranar 23 ga watan Yunin 2026.

An sauya alkali a shari'ar ADC

A wani labari, mun ruwaito cewa, Babban Alkalin Kotun Tarayya ta sauya alkalin da ke jagorantar shari'ar rikicin shugabanci a jam'iyyar ADC.

Kotun ta mayar da karar da Nafiu Bala ya shigar kan shugabancin ADC zuwa wani sabon alkali domin ci gaba da sauraron shari'ar.

Nafiu Bala na neman hana David Mark da Rauf Aregbesola tare da kwamitin rikon kwarya gudanar da ayyukan shugabancin jam'iyyar ADC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com