Martanin Kwankwaso bayan Samu Tikitin Takarar Mataimakin Peter Obi a NDC

Martanin Kwankwaso bayan Samu Tikitin Takarar Mataimakin Peter Obi a NDC

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi martani bayan NDC ta tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027
  • Kwankwaso ya bayyana farin cikinsa da wannan dama, yana mai cewa amincewar da jam'iyyar da Peter Obi suka nuna masa babban abin alfahari ne
  • Tsohon gwamnan Kano ya yabawa Sanata Seriake Dickson da shugabannin NDC, yana cewa matakin ya nuna ƙudirin haɗin kai da ƙarfafa dimokuraɗiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi martani bayan nasarar samun tikitin takarar mataimakin shugaban kasa a NDC.

Jam'iyyar ta tsayar da Peter Obi a matsayin wanda zai yi mata takara a zaben shgaban kasa inda ya zabi Kwankwaso a matsayin mataimakinsa.

Kwankwaso ya magant bayan samun takara a NDC
Peter Obi tare da Sanata Rabiu Kwankwaso a taron jam'iyyar NDC a Abuja. Hoto: @SaifullahiHon.
Source: Twitter

Legit Hausa ta samu bayanin tsohon gwamnan Kano ne a shafinsa na X wanda ya wallafa da safiyar yau Lahadi 31 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya san matsayinsa da Peter Obi ya ayyana abokin takararsa na zaben 2027

Kwankwaso ya yi farin cikin samun tikitin NDC

Kwankwaso ya ce ya ji matukar farin ciki da samun wannan dama wanda jam'iyyar NDC da Peter Obi ba shi game da zaben 2027.

Tsohon gwamnan ya yi godiya na musammnan ga shgabanni da mambobin jam'iyyar mai adawa bisa wannan karramawa da aka yi masa.

Ya ce:

"Na ji matuƙar farin ciki da girmamawa kasancewata tare da sauran mambobin jam'iyya a taron musamman na tabbatar da Mai Girma Peter Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Nigerian Democratic Congress (NDC) domin babban zaɓen shekarar 2027.
Hakazalika, na ji matuƙar ƙasƙantar da kai da kuma jin daɗin girmamawar da aka yi min ta hanyar tabbatar da ni a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar."
Kwankwaso ya godewa Obi da shugabannin NDC
Peter Obi tare da Sanata Rabiu Kwankwaso a taron jam'iyyar NDC a Abuja. Hoto: @SaifullahiHon.
Source: Twitter

Godiya ta musamman da Kwankwaso ya yi

Sanata Kwankwaso ya kuma tura godiyarsa ta musamman ga jagoran NDC, Sanata Seriake Dickson wanda ya aminta da shi kan wannan matsayi.

Ya ce wannan mataki da aka dauka ya tabbatar da kudirin NDC na samar da hadin kai da karfafa dimukradiyya domin samar da shugabanci mai nagarta.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Atiku ya girma, ya samu tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2027

"Ina miƙa godiyata ta musamman ga jagoran NDC na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, da sauran shugabannin jam'iyyar bisa wannan jarumtacciyar shawara mai hangen nesa.
"Wannan mataki ya ƙara nuna ƙudirin NDC na tabbatar da haɗin kan ƙasa, ƙarfafa dimokuraɗiyya da samar da shugabanci mai ma'ana yayin da muke shirye-shiryen tunkarar zaɓen shekarar 2027."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya ba Aminu Gwarzo tikitin takara

A wani labarin, an ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya sanar da cewa a yau Juma'a, 29 ga Mayun 2026 za su kaddamar da 'yan takarar da za su wakilci NDC a 2027.

Kwankwaso ya ayyana tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo a matsayin wanda zai yi wa NDC takarar gwamnan Kano.

Ya kuma fadi matsayin da tsohon mataimakin gwamnan Kano, Dr Nasiru Yusuf Gawuna zai nema a karkashin tafiyar NDC Kwankwasiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.