Sojoji Sun Gwabza da Yan Bindiga karkashin Aleiro, An Kashe Rayuka a Zamfara
- Dakarun Operation Fansan Yamma sun yi artabu da mayaƙan Ado Allero inda aka dauki tsawon lokaci ana dauki ba dade a jihar Zamfara
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an dauki lokaci ana musayar wuta, lamarin da ya jawo mutuwar wasu da yawa yayin da wasu su ka samu raunuka
- Sojoji su na ci gaba da akin farautar fitinannun yan ta'addan da su ka addabi jama'a yayin da ake dakon wasu muhimman bayanai daga rundunar sojin kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma na ci gaba da fafatawa da mayaƙan fitaccen jagoran 'yan bindiga Ado Allero a wani sabon samame da suka kai a yankin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Majiyoyin tsaro sun shaida cewa artabun ya fara ne bayan dakarun sun yi karo da 'yan bindigar yayin wani farmaki da ake gudanarwa domin tarwatsa ayyukan ƙungiyar.

Source: Twitter
Jaridar Zagazola Makama ta wallafa cewa rahotanni sun ce an kashe 'yan bindiga da dama a yayin musayar wutar, sai dai har yanzu ana jiran wasu muhimman bayanai.
Rahotannin sun ce dakarun sun yi amfani da manyan makamai wajen fuskantar 'yan bindigar, waɗanda ake zargin sun fito da yawa kuma suna ɗauke da muggan makamai
Zargin da ake wa Aleiro da yaransa
Rahoton ya ce Ado Allero na daga cikin fitattun shugabannin 'yan bindiga da hukumomin tsaro ke nema ruwa a jallo saboda rashin imanin da su ke aikatawa.
Ana zarginsa da jagorantar hare-hare, satar mutane domin neman kuɗin fansa da kuma satar shanu a wasu sassan jihohin Zamfara, Katsina da maƙwabtansu.

Source: Original
Rundunonin tsaro sun sha kai hare-hare kan sansanoninsa a ƙarƙashin Operation Fansan Yamma, da nufin rushe mafakar 'yan ta'adda da 'yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.
Wata majiya ta bayyana cewa fafatawar tana da tsanani matuƙa, inda aka ce ana kuma shirin tura ƙarin dakaru tare da amfani da sa ido ta sama idan buƙatar hakan ta taso.

Kara karanta wannan
'Ba Abuja ba ne,' 'Yan sanda sun gano jihar da 'yan ta'adda suka kashe babban soja
Ana jiran bayan sojoji kan Aleiro
Duk da rahoton cewa an kashe 'yan bindiga da yawa, zuwa wannan lokaci rundunar sojin Najeriya ko wasu majiyoyi ba su bayyana adadin waɗanda aka kashe ko asarar da aka yi daga ɓangarorin biyu ba
Ana sa ran hukumomin soji za su fitar da ƙarin bayani yayin da ake ci gaba da wannan aiki inda ake cewa akwai sauran jami'an tsaro ana aiki a yankin.
Wannan arangama na daga cikin kokarin da sojoji su ka rubanya wajen yaki da yan bindiga da dangogin laifuffukan da ake tafkawa a Arewa maso Yamma.
Sojoji sun fara farautar Dogo Gide
A baya, kun samu labarin cewa dakarun Operation Fansan Yamma sun fara kai hari tare da neman fitinannun 'yan bindiga da su ka addabi mazauna jihar Zamfara da kewaye na tsawon lokaci.
Harin sama da na ƙasa sun tarwatsa yunkurin taruwar ɗaruruwan ‘yan bindiga tare da kashe da dama daga cikinsu a lokacin da su ke tattaunawa kan yadda za su kai wa jama'a hari ba gaira ba dalili.
Sojojin sun samu nasarar kwato harsasai yayin da dakaru ke ci gaba da sintiri domin hana ‘yan bindiga sake samun mafaka a yankin da kuma kara tsaurara tsaro da sa ido domin samun nasarar aiki
Asali: Legit.ng
