Gawuna da Gwarzo: Kwankwaso Ya Fitar da Dan Takarar Gwamnan Kano na 2027

Gawuna da Gwarzo: Kwankwaso Ya Fitar da Dan Takarar Gwamnan Kano na 2027

  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya sanar da cewa a yau Juma'a, 29 ga Mayun 2026 za su kaddamar da 'yan takarar da za su wakilci NDC a 2027
  • Kwankwaso ya ayyana tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo a matsayin wanda zai yi wa NDC takarar gwamnan Kano
  • Ya kuma fadi matsayin da tsohon mataimakin gwamnan Kano, Dr Nasiru Yusuf Gawuna zai nema a karkashin tafiyar NDC Kwankwasiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Magudun Kwakwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da manyan wadanda za su yi wa NDC takara a Kano.

Rabiu Kwankwaso ya bayyana haka ne a daren Alhamis, 28 ga watan Mayu, yayin da hankali ya karkata kan 'yan takarar da zai tsayar.

Manyan yan siyasar NDC a Kano
Rabiu Kwankwaso, Aminu Gwarzo da Yusuf Gawuna a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Hadimin Sanata Rabiu Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya sanar da cewa a yau Juma'a, 29 ga Mayun 2026 za a kaddamar da 'yan takarar a wani sako da ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

"Ko Ganduje ba zai ce shi ba yarona ba ne": Kwankwaso ya yi martani ga Abba

Rabiu Kwankwaso ya fitar da 'yan takara

Sanata Rabiu Kwankwaso ya sanar da cewa Aminu Abdulsalam Gwarzo da ya ajiye kujerar mataimakin gwamnan Kano bayan Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka ne zai masu takarar gwamna a NDC a 2027.

Ya fadi haka yayin da ya gana da wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar NDC da Kwankwasiyya a Kano game da batun siyasar jihar da Najeriya baki daya.

Kwankwaso ya kuma tabbatar da cewa Nasiru Yusuf Gawuna zai nemi Sanata a Kano yayin da Peter Obi zai yi wa NDC takarar shugaban kasa.

Nasiru Gawuna zai yi takarar kujerar Kano ta tsakiya tare da Malam Ibrahim Shekarau a zaben 2027.

Jawabin Kwankwaso bayan cinma matsaya

Ga sakon da hadimin Kwankwaso ya wallafa game da batun takarar:

"Yayin da ake dakon taron tabbatar da ’yan takara gobe (Yau Juma'a), Mai Girma Jagora Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana Aminu Abdulsalam Gwarzo a matsayin ɗan takarar Gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

NDC: An gano wanda Kwankwaso ke so ya tsayar ya fafata da Abba a Kano

" Mai Girma Alhaji Dr Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, tare da bayyana Mai Girma Peter Obi a matsayin ɗan takarar shugaban kasa.
Allah maɗaukakin sarki Ya sanya alheri a wannan tafiya, ya ba su nasara, ya tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa da Jihar Kano baki ɗaya. Amin"

Bayan tabbatar da 'yan takarar da za su wakilci jam'iyyar NDC a jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya fitar da sanarwar tabbatar da hakan a shafinsa na X.

Ya ce:

"Ina farin cikin sanar da cewa an zabi mai girma, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a jihar Kano a zabe mai zuwa.
"Haka kuma, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna zai tsaya takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya."
Sanata Rabiu Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso na bayani a gidan shi da ke Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Maganar Kwankwaso kan Ganduje

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi martani ga wasu 'yan siyasar da ke cewa su ba yaran shi ba ne a Kano.

Ya bayyana cewa rashin kunya ce za ta saka mutane irin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje cewa su ba yaran shi ba ne a siyasa.

A kwanakin baya ne Abba Kabir Yusuf ya fusata yana cewa bai kamata Kwankwaso ya rika kiran shi da yaro ba, saboda shi ma ya haura shekara 60.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng