Dakarun Gandun Daji: Tinubu Amince a Dauki Sababbin Ma'aikata 1,000 a Katsina

Dakarun Gandun Daji: Tinubu Amince a Dauki Sababbin Ma'aikata 1,000 a Katsina

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da bukatar Gwamnatin Katsina na daukar dakarun gandun daji 1,000 domin karfafa tsaro a dazuzzukan jihar
  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya ce malaman addini da al’umma na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen dakile ayyukan ‘yan bindiga
  • Gwamnatin Katsina ta haramta amfani da babura, POS da sayar da man fetur a wasu yankuna domin takaita ayyukan 'yan ta'adda a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Katsina - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da daukar matasa 1,000 a matsayin dakarun gandun daji domin taimakawa kokarin dakile matsalar tsaro a jihar Katsina.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin da yake ganawa da manema labarai bayan wata tattaunawa da malaman addinin Musulunci da sauran masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati da ke jihar.

Kara karanta wannan

Ran shugaban gwamnonin Arewa ya baci kan surutu babu aiki, ya kawo mafita

Tinubu ya bada umarni a dauki dakarun gandun daji 1,000 a Katsina.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (hagu) da Gwamna Dikko Umaru Radda (dama). Hoto: @DOlusegun, @Miqdad_Jnr
Source: Twitter

Gwamnan Katsina ya nemi gudunmawar malamai

An gudanar da taron ne domin tattauna hanyoyin da al’umma za su taka rawa wajen magance matsalolin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, in ji rahoton Daily Trust.

Gwamna Radda ya ce manufar ganawar ita ce jin ra’ayoyin malaman addini kan matsalar tsaro da kuma samun shawarwari kan hanyoyin samar da mafita mai dorewa.

Ya bayyana cewa yaki da ‘yan bindiga ba aiki ne da hukumomin tsaro kadai za su iya yi ba, domin al’umma ma na da muhimmiyar rawa wajen magance matsalar.

A cewarsa, bincike ya nuna cewa wasu daga cikin mazauna yankuna na taimakawa masu aikata laifuka ta hanyar ba su bayanai ko kuma taimakawa wajen sayar da dabbobin da suka sata.

“Yawancin suna samun kayayyaki da bayanan da suke amfani da su ne daga wasu mutane da ke rayuwa tare da mu. Saboda haka akwai bukatar wayar da kan jama’a domin kowa ya taka rawarsa,” in ji Dikko Radda.

Kara karanta wannan

Tsaro: An kafa zafafan dokoki a Katsina, an hana POS, cajin waya da sauransu

Matakan gwamnati kan matsalar tsaro

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta dauki wasu matakai masu tsauri domin rage ayyukan ‘yan bindiga a wasu yankunan da matsalar ta fi kamari, a cewar rahoton Legit Hausa.

Ya ce an haramta amfani da babura a kananan hukumomi kamar Musawa da Matazu, tare da takaita amfani da na’urorin POS da wuraren cajin wayoyi da ake zargin suna taimakawa ayyukan masu laifi.

Haka kuma ya bayyana cewa an sanya takunkumi kan sayar da man fetur a wasu yankuna domin rage damar da kungiyoyin masu dauke da makamai ke da ita wajen gudanar da ayyukansu.

Gwamna Dikko Radda ya ce dakarun gandun daji za su taimaka wajen dakile matsalar tsaro a Katsina.
Wasu dakarun gandun daji da ke aikin tsaro a dazuzzuka. Hoto: LESLIE FAUVEL / Contributor
Source: Getty Images

Tinubu ya kara tura jami’an tsaro Katsina

Da yake yabawa Gwamnatin tarayya, Radda ya gode wa Shugaba Tinubu bisa amincewa da bukatar jihar na daukar dakarun gandun daji 1,000, in ji rahoton Punch.

Ya ce za a horar da matasan tare da ba su kayan aiki domin su yi aiki tare da jami’an tsaro da kungiyoyin sa-kai wajen kare yankunan karkara da dazuka.

Kara karanta wannan

Yadda aka karbo gawar Manjo Janar Rabe Abubakar bayan ya rasu a hannun 'yan Bindiga

Gwamnan ya kuma yaba da karin jami’an soja, ‘yan sanda da jami’an DSS da gwamnatin tarayya ta tura jihar domin karfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Gidan rediyon alfijir ya wallafa tattaunawar gwamnan jim kadan bayan ganawarsa da malaman addinin a shafinsa na Facebook.

Kalli hirar a nan kasa:

'Yan sanda sun dauki sabon mataki a Katsina

A wani labari, mun ruwaito cewa, Sufeto Janar na Najeriya, Olatunji Disu, ya umarci rundunar 'yan sandan Katsina ta ƙara tsaurara matakan tsaro a jihar.

Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da Kuɗi da Gudanarwa, Sulaiman Abdul, ya isar da umarnin yayin rangadin aiki na kwanaki biyu.

Jami’an sun duba katanga, wuraren shiga da fita, guraben tsaro da kuma tattaunawa da shugabannin makarantu kan matsalolin tsaro da hanyoyin magance su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com