Tsugune ba Ta Ƙare ba, Ana Kokwanton Zaben Amaechi a matsayin Mataimakin Atiku

Tsugune ba Ta Ƙare ba, Ana Kokwanton Zaben Amaechi a matsayin Mataimakin Atiku

  • Jam'iyyar ADC ba ta tabbatar da rahotannin da ke cewa an zabi Rotimi Amaechi a matsayin mataimakin Atiku Abubakar ba
  • Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa ba shi da bayanin da zai tabbatar ko karyata batun zaben Amaechi
  • Rahotanni sun ce tikitin Atiku da Amaechi zai iya karfafa ADC a Kudu maso Kudu kafin babban zaben 2027 da ake tunkara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam'iyyar ADC ta ki tabbatar da rahotannin da ke cewa an zabi mataimakin dan takarar shugaban kasa ba.

Rahotannin da kafafen yada labarai sun wallafa cewa Atiku Abubakar ya amince da Rotimi Amaechi a matsayin mataimakinsa a zaben 2027.

ADC ta ko tabbatar da zaben Amaechi a matsayin mataimakin Atiku
Dan takarar shugaban ƙasa a ADC, Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi. Hoto: Atiku Abubakar, Rt. Hon. Rotimi Amaechi.
Source: Twitter

ADC ta magantu kan zaben Amaechi mataimakin Atiku

Sai dai a wata hira da Premium Times, sakataren yada labarai na ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce ba zai iya tabbatar da rahotannin ba.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Peter Obi ya bayyana abin da zai fara yi game da Nnamdi Kanu

Ya ce:

"Ba ni da wannan tabbacin, ba zan iya tabbatar da hakan a wannan lokaci ba."

Da aka tambaye shi ko ana ci gaba da tattaunawar zaben mataimakin shugaban kasa, Abdullahi ya ki bayar da karin bayani kan lamarin.

Ya ce abin da zai iya fada kawai shi ne ba shi da bayanin da zai tabbatar da batun da aka tambaye shi.

Sai dai ya tabbatar da cewa jam'iyyar za ta sanar da wanda zai zama mataimakin dan takarar shugaban kasa idan lokaci ya yi.

Ya ce:

"Tabbas za mu samu mataimakin shugaban kasa. Amma dangane da tambayar da ka yi, ba zan iya tabbatar da hakan yanzu ba."

Hasashen yiwuwar tikitin Atiku da Amaechi ya karu bayan Atiku ya lashe zaben fitar da gwani na ADC gaban Amaechi da sauran masu neman takara.

An yada cewa Atiku ya zaɓi Amaechi a matsayin mataimakinsa
Tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriya, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Tasirin da zaben Amaechi zai yi ga Atiku

Rahotannin sun nuna cewa Atiku daga Adamawa na iya hade da Amaechi daga Ribas domin samar da tikitin Arewa maso Gabas da Kudu maso Kudu.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalam ya faɗi abin da ba a sani ba kan mutuwa fuju'a da Abiola ya yi

Idan aka tabbatar da hakan, za a hada manyan 'yan siyasa biyu masu tasiri da suka taba aiki a gwamnatin Muhammadu Buhari.

Lamarin ya kara daukar hankali bayan jigo a jam'iyyar ADC, Chukwuemeka Eze, ya musanta rade-radin cewa Amaechi ya ki amincewa da mukamin mataimaki.

Eze na mayar da martani ne ga kalaman da aka danganta wa Dele Momodu cewa Amaechi ba ya son karbar mukamin mataimakin shugaban kasa.

A wata sanarwa, Eze ya ce babu hujjar cewa Amaechi ya yi watsi da wata tayi, domin ya ce babu wanda ya tuntube shi kan batun.

Masu sa ido kan harkokin siyasa sun kwatanta wannan lamari da abin da ya faru a 2023 lokacin da Atiku ya zabi Ifeanyi Okowa bayan ya doke Nyesom Wike.

Sun ce zaben Amaechi, idan aka tabbatar da shi, zai iya kara wa ADC karbuwa a yankin Kudu maso Kudu, cewar Daily Post.

Atiku ya magantu kan ta'addanci a Najeriya

Mun ba ku labarin cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya yi murna da ceto mutum 360 da aka sace a Ngoshe da ke jihar Borno.

Kara karanta wannan

ADC: Rahoto ya nuna mutumin da Atiku zai dauka mataimaki a zaben 2027

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yabawa sojoji da jami’an tsaro kan nasarar da suka samu na ceto mutanen bayan watanni fiye da biyu.

Ya ce hakan ya nuna cewa dakarun tsaron Najeriya za su iya magance duk wata barazana matukar aka samar masu da kayan aiki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.