NDC Ta Fara Lallaba Sanata Hanga da Kabiru Gaya bayan Hango Su da Tinubu

NDC Ta Fara Lallaba Sanata Hanga da Kabiru Gaya bayan Hango Su da Tinubu

  • NDC ta yi martani ga zargin da ake yi na cewa Sanata Rufa'i Hanga da tsohon gwamna Kabiru Ibrahim Gaya za su iya barin NDC
  • A cikin ƴan kwanakin nan, ana ganin yadda manyan jagororin ke tattaunawa da shugabannin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
  • Jam'iyyar ta ce har yanzu tana kallon Sanata Hanga da Gaya a matsayin mambobinta duk da ganawarsu da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jam'iyyar NDC ta bukaci Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga, da tsohon gwamnan Kano, Kabiru Ibrahim Gaya, da su sake tunani kan rade-radin da ke cewa suna shirin komawa jam'iyyar APC.

Kiran ya biyo bayan ziyarar da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, tare da Hanga da Gaya suka kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja ranar Lahadi, 26 ga watan Yuli, 2026.

Kara karanta wannan

Sanata na kusa da Kwankwaso ya fara neman barin NDC a Kano

Ana neman Hanga da Gaya su hakura da APC
Sanata Rufa'i Hanga, Barau I Jibrin, tsohon gwamna Kabiru Gaya, da Bola Tinubu a Abuja Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa yadda shugaban APC na kasa ya kai ziyara gidajen Hanga da Gaya, lamarin da ya kara tayar da jita-jitar cewa suna dab da sauya sheka.

Kiran NDC ga Hanga da Gaya

Shugaban NDC na jihar Kano, Hussaini Isah Mairiga, ya shaida wa Daily Trust cewa jam'iyyar ta damu da rahotannin da ake yadawa kan sauya shekar manyan siyasar biyu.

Ya ce:

"Labarin cewa APC mai mulki na kokarin jan hankalin Sanata Rufai Sani Hanga da tsohon gwamnan Kano Kabiru Gaya ya bazu ko'ina. Har yanzu ba su sanar da mu a hukumance cewa za su sauya sheka ba, amma jiya ma mun gan su sun ziyarci Shugaba Tinubu. Wannan na nuna cewa labarin na iya zama gaskiya."

Mairiga ya ce jam'iyyar ba za ta ji dadin rasa irin wadannan manyan jiga-jigai ba saboda haka su yi hakuri, su yi zamansu a NDC.

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Ana neman ruguza Kwankwaso a Kano, Barau ya kai Hanga wajen Tinubu

"A matsayinmu na shugabanni, ba za mu yi farin ciki idan suka sauya sheka ba. Ko mamba na gari ya fita ba ma jin dadi, balle irin wadannan manyan mutane. Muna da kyakkyawar alaka da su kuma muna girmama juna."

NDC ta roki su Hanga

Mairiga ya amince cewa Hanga ya taba nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake tafiyar da wasu al'amura a cikin NDC, amma ya ce jagoran jam'iyyar, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zabi kada ya mayar masa da martani nan take.

NDC ta Ce har yanzu ana buƙatar Gaya da Hanga a cikinta
Jagoran NDC na kasa, Seriake Dickson Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

A cewarsa:

"Tun da ba su sanar da sauya shekar ba a hukumance, muna rokon su su sake tunani su dakatar da wannan shiri. Mu zauna mu tattauna idan akwai abin da muka yi musu ba daidai ba."
"Kwankwaso ya ce bai ba shi amsa ba ne saboda yana cikin fushi, don haka ya jira ya huce kafin su zauna su tattauna."

Duk da kusancin da jam'iyyar APC mai mulki ke nunawa Sanata Hanga da Gaya, shugaban NDC na Kano ya ce har yanzu mutanen biyu cikakkun ƴaƴanta ne.

Hanga na dab da barin NDC

A baya, kun samu labarin cewa Sanata Rufai Sani Hanga ya fara tuntubar masu ruwa da tsaki a Kano ta Tsakiya yayin da ake rade-radin cewa yana shirin ficewa daga NDC.

Kara karanta wannan

Bayan shekara a APC, Sanata ya koma tsohuwar jam'iyyarsa

Hanga ya gana da shugabannin APC da Gwamna Abba Kabir Yusuf, sannan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin kuma ya ga Bola Tinubu.

Kungiyar Kwankwasiyya ta ce ba za ta damu ba idan Hanga ya sauya sheka, tana mai cewa an ba shi tikitin takara ba tare da hamayya ba a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng