An Daura Auren Gata ga Mutum 300 a Kebbi, Gwamnati za Ta Cigaba da Shirin

An Daura Auren Gata ga Mutum 300 a Kebbi, Gwamnati za Ta Cigaba da Shirin

  • Gwamnan Jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da gudanar da shirin auren gata na shekara-shekara
  • Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da aka ɗaura auren ma'aurata 300 a Birnin Kebbi, inda ya ce shirin zai ci gaba a duk tsawon mulkinsa
  • Mai ɗakin gwamnan, Hajiya Nafisa Idris, ta ce gidauniyarta ce ta ƙirƙiri shirin domin rage wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi nauyin kashe kuɗin aure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Birnin Kebbi – Gwamnan Jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da gudanar da shirin auren gata na shekara-shekara domin tallafa wa marasa galihu a faɗin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin bikin ɗaura auren ma'aurata 300 da aka gudanar a filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta hango kura kurai a kalaman Obi, ta yi masa zazzafan martani

Wajen aure gata a Kebbi
Wadanda aka yi wa auren gata a jihar Kebbi. Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa gwamnan ya ce shirin ya zama wani muhimmin tsari na jin ƙai da ke taimakawa iyalai masu ƙaramin ƙarfi wajen rage musu nauyin kashe kuɗin aure.

Za a cigaba da irin auren

Dr Nasir Idris ya ce zai ƙara ƙaimi wajen tabbatar da cewa mutane masu ƙaramin ƙarfi suna ci gaba da cin gajiyar wannan shiri.

Ya ce:

"Zan ci gaba da ƙara ƙoƙari a wannan shiri domin tabbatar da cewa ƙarin marasa galihu sun amfana da shi."

Gwamnan ya kuma yaba wa mai ɗakinsa, Hajiya Nafisa Idris, bisa jagorantar shirin ta hanyar gidauniyarta, yana mai cewa hakan babban gudunmawa ne ga jin daɗin al'ummar jihar.

Ya kuma yi kira ga al'ummar Kebbi da su ci gaba da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC baya, yana mai cewa manufofin shugaban sun kawo ci gaba mai ma'ana ga jihar.

A cewarsa:

"Ni na kasance cikin mafi farin ciki a yau saboda wannan taro ya nuna cewa mutanen Jihar Kebbi suna goyon bayan shugaban ƙasa. Muna nan daram a APC."

Kara karanta wannan

Najeriya ta saye sababbin jiragen yaki, za a zafafa yakar 'yan ta'adda

Abin da matar gwamna ta ce

Hajiya Nafisa Nasir Idris ta bayyana cewa gidauniyarta ce ta ƙaddamar da shirin auren gata domin taimaka wa marayu, zawarawa da sauran masu buƙata tare da rage musu nauyin kashe kuɗin aure.

Ta tabbatar da cewa za a ci gaba da gudanar da shirin tare da gode wa mutane da ƙungiyoyin da suka ba da gudunmawa wajen nasarar sa.

Gwamnan Kebbi a wajen taro
Gwamna Nasir Idris yana zaune a ofis. Hoto: Dr Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Ta kuma shawarci sabbin ma'auratan da su ji tsoron Allah, su riƙe koyarwar addinin Musulunci, sannan su gina gidajensu bisa mutunta juna, haƙuri da fahimtar juna.

'Yar shugaban ƙasa, Dakta Mujidat Tinubu-Ojo, ta yaba da shirin, tana mai cewa yana taimaka wa marasa galihu, tare da ƙarfafa sababbin ma'auratan su yi rayuwa bisa koyarwar Annabi Muhammad (SAW).

An biya sadaki ga amare 300

An gudanar da ɗaura auren ne bisa koyarwar addinin Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sheikh Imam Mukhtar tare da sauran malamai.

A yayin bikin, Gwamna Nasir Idris ya biya sadakin N200,000 ga kowace amarya daga cikin amaren 300, sannan aka yi addu'o'in neman zaman lafiya da albarka ga sabbin ma'auratan.

Kara karanta wannan

Kai mutane Hajji, taimakon almajirai da ayyukan Peter Obi a Arewa

Shi ma Kwamandan Hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Daurawa, wanda ya halarci bikin, ya yaba da shirin a Facebook, yana mai cewa:

"Alhamdulillah. An gudanar da taron auren gata na ma’aurata 300 a Jihar Kebbi, wanda ya haɗa da waɗanda suka cika sharudan shirin.
"Wannan ya kasance wani shiri na tallafa wa marayu, zawarawa da sauran masu buƙatar taimako wajen kafa ingantattun gidaje."

An yanke azzakarin saurayi

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wata mata mai shekara 25 bisa zargin yanke mazakutar saurayinta bayan ta gano yana shirin auren wata.

Rundunar ta ce lamarin ya faru ne a wani otal, inda aka garzaya da wanda aka jikkata asibiti domin samun kulawar likitoci, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama matar ne bayan jami'ai sun kai ɗauki cikin gaggawa bayan samun rahoton abin da ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng