Mataimakin Gwamnan Kano Ya Haifar da Ruɗani a Rikicin Sarauta tsakanin Aminu Ado da Sanusi II

Mataimakin Gwamnan Kano Ya Haifar da Ruɗani a Rikicin Sarauta tsakanin Aminu Ado da Sanusi II

  • Mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, ya halarci Mauludin Sheikh Ahmad Tijjani, wanda aka gudanar a fadar Aminu Ado Bayero
  • An gudanar da taron ne a daidai lokacin da takaddamar masarautar Kano ke ci gaba tsakanin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II
  • Masu halartar Mauludin sun nuna damuwa kan rashin amincewa da amfani da filin wasa na Sani Abacha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Mataimakin gwamnan jihar Kano, Murtala Sule Garo, ya halarci Mauludin Sheikh Ahmad Tijjani na shekara-shekara da aka gudanar a fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ranar Lahadi.

Taron ya samu halartar malamai, mabiya darikar Tijjaniyya da sauran masu ibada daga Kano da jihohin makwabta, har ma da yan kasashen waje.

Garo.
Mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo ya halarci taron Maukidi a fadar Aminu Ado Bayero Hoto: Masarautar Kano
Source: Facebook

Jaridar Punch ta rahoto cewa an gudanar da taron ne a daidai lokacin da takaddamar sarautar Kano tsakanin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II ke ci gaba.

Kara karanta wannan

Yadda za a sabunta fadar sarkin Gombe ta zama ta yi zarra a Arewa

Murtala Garo ya halarci taron Sarki Aminu

Halartar Garo ta dauki hankali saboda Aminu Bayero da Sanusi na ci gaba da kasancewa a tsakiyar rikicin masarautar Kano.

Aminu Ado Bayero na samun goyon bayan wani bangare da ke da alaka da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, yayin da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke goyon bayan Muhammadu Sanusi II.

An gudanar da Mauludin a fadar Nasarawa inda Aminu Ado ke zaune duk da cewa gwamnatin jihar ta amince da Sanusi II a matsayin sarki bayan dawo da shi kan karagar mulki a watan Mayun 2024.

An gudanar da Mauludi a fadar Bayero

A baya, an yi yunkurin gudanar da Mauludin a filin wasa na Sani Abacha, amma rahotanni sun nuna cewa ba a samu amincewar gwamnatin jihar cikin lokaci ba.

A nasa bangaren, kakakin Sarki Aminu Ado Bayero, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa, ya ce mataimakin gwamnan ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen taron.

Kara karanta wannan

Da gaske Sarki Sanusi II ya fadi jarabawa da ya koma karatu jami'a a Kano?

Sai dai ya bayyana cewa mutanen da suka raka mataimakin gwamnan ba jami’an gwamnati ba ne, illa dai wasu daga cikin magoya bayansa.

Kofar Na’isa ya ce masu shirya Mauludin sun rubuta wa ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano da kuma na mai ba gwamnan shawara kan harkokin addini domin neman izinin amfani da filin wasan Sani Abacha, amma hakan ba ta samu ba.

Aminu Ado.
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero tare da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume a wurin Maulidi a fadar Nasarawa Hoto: Masarautar Kano
Source: Facebook

Mauludin ya tara dumbin mutane

Wani mazaunin Kano, Ilyasu Idris, ya ce taron ya nuna cewa darikar Tijjaniyya na ci gaba da samun dimbin mabiya a jihar.

Ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne an gudanar da Mauludin cikin kwanciyar hankali, inda mutane suka samu damar haduwa domin addu’o’i da sauran ayyukan ibada.

Jawabin Tinubu a Maulidin Sheikh Tijjani

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura wakili wurin maulidin Sheikh Ahmad Al-Tijani, RTA, wanda ya gudana a jihar Kano.

A jawabin da ya tura, Tinubu ya bukaci shugabannin Tijjaniyya da mabiyansu na duniya su fito su rika sukar ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.

Ya kuma bukaci kungiyoyin addini da hanyoyin sadarwarsu su kara karfafa wayar da kan jama’a kan zaman lafiya, ilimin addini, karatu da kuma tarbiyyar matasa masu nagarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262