Majalisa Ta Karyata Alkawarin da aka Ce Akpabio Ya Yi wa Sanatocin da Suka Fadi Zabe
- Majalisar Dattawa ta yi magana game da alkwarin da aka ce shugabanta, Godswill Akpabio ya yi wasu sanatocin
- Rahotanni a baya sun bayyana cewa majalisa za ta duba wasu daga cikin sanatocin da suka fadi zaben fitar da gwani
- Akpabio ya ce ya nuna tausayi ne kawai ga wadanda suka sha kaye, ya ce APC na kokarin warware matsalolin da suka taso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ofishin Shugaban Majalisar Dattawa ya warware rashin fahimta da aka samu game da alkawarin da aka ce Godswill Akpabio ya yi.
Ofishin ya karyata rahotannin da ke yawo cewa ya yi wa sanatocin da suka fadi a zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC alkawarin tabbatar masu da tikitin takara.

Source: Facebook
Punch ta labarto cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da Mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama'a, Eseme Eyiboh, ya fitar ranar Asabar, 6 ga watan Yuni, 2026.
Majalisa ta yi bayani game da kalaman Akpabio
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa sanarwar Eseme Eyiboh ta tabbatar da cewa rahotannin da aka fitar game da alkawarin sun juya kalaman Akpabio.
Sanarwar ta ce Shugaban Majalisar Dattawar bai taba yin alkawarin samar wa sanatocin da zaben fitar da gwani ya shafa tikitin takara ba.
Ta kara da cewa haka kuma Gpdswill Akpabio a bai ba kowa izinin yin irin wannan alkawari a madadinsa ba.

Source: Facebook
A cewar Eyiboh, abin da Akpabio ya yi shi ne nuna tausayi ga sanatocin da sakamakon gaza kai labari a zaben fitar da gwani.
Ya kuma ba su tabbacin cewa shugabancin APC na aiki domin magance dukkannin matsalolin da suka taso bayan zaben.

Kara karanta wannan
Da gaske 'yan bindiga sun sako dalibai da malamai da suka sace a Oyo? Bayanai sun fito
Za a fitar da yan takarar APC - Akpabio
A cewar Eyiboh, Akpabio ya kuma sanar da sanatocin cewa za a fitar da jerin sunayen 'yan takarar jam'iyyar na karshe a lokacin da ya dace bisa tanade-tanaden kundin tsarin APC da kuma dokokin zabe.
Eyiboh ya jaddada cewa Akpabio na mutunta dokokin jam'iyya, bin hanyoyin da suka dace da kuma tsarin sasanta rikice-rikice na cikin gida na APC.
Ya ce ba zai tsoma baki a harkokin da jam'iyyar ke da ikon tafiyar da su da kanta ba, ko kuma ya yi alkawuran da ba sa cikin ikon shugabancin Majalisar Dokoki.
Ya bukaci 'yan jarida da jama'a su yi watsi da rahotannin da ya kira marasa tushe, tare da neman karin haske daga ofishinsa kafin wallafa labaran da suka shafi kalaman da ya yi.
Akpabio ya yi magana kan barazana ga Arewa
A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio bai yi kalaman rashin da'a ko barazana da 'yan Arewa gabanin zaben 2027 ba.

Kara karanta wannan
An fara jita jitar cewa Sheikh Abdulmudallib ya samu tikitin takarar gwamna a 2027
Ofishin shugaban majalisar ya yi fatali da wani faifan bidiyo da ake yadawa a kafafen sada zumunta, ya ce karya ce tsagwaronta da ke neman yamutsa hazo gabanin zaben.
Ya buƙaci ‘yan Najeriya, musamman mutanen Arewa, su yi watsi da zargin cewa ya fada masu magana tare da gujewa duk wani abu da zai wargaza hadin kan da ake da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
