Akpabio: Majalisar Dattawa za Ta Ceto Sanatocin APC da aka Kwarfe

Akpabio: Majalisar Dattawa za Ta Ceto Sanatocin APC da aka Kwarfe

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi magana kan sanatocin da suka gaza samun tikitin jam’iyyunsu a zabukan fitar da gwani na baya-bayan nan
  • Akpabio, wanda ya samu tikitin jam’iyyar APC ya ce shugabancin majalisar dattawa ya yi tsammanin sanatoci kaɗan ne kawai za su rasa damar sake tsayawa takara
  • Ya bayyana cewa shugabancin majalisar na nazarin hanyoyin da za a bi domin magance wasu daga cikin sakamakon zabukan fitar da gwanin tare da taimaka wa sanatocin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce majalisar na kokarin ganin an samar wa wasu sanatocin da suka kasa samun tikitin tsayawa takara a zabukan fidda gwani damar komawa takara a 2027.

Hakan na zuwa ne bayan korafe-korafe sun yawaita a jam'iyyar APC kan faduwa zaben fitar da gwani da kuma zargin magudi a zaben.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio
Godswill Akpabio na bayani a majalisar dattawa. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa kusan sanatoci 40 daga jam’iyyu daban-daban da suka hada da APC, PDP da NDC, da sauransu, sun sha kaye a zabukan fitar da gwani.

Kara karanta wannan

NDC: Jam'iyyar su Obi ta rikice kan zaɓen fitar da gwani a jihar Delta

Maganar da Akpabio ya yi

Da yake jawabi bayan dawowar Majalisar Dattawa daga hutun makonni hudu, Akpabio ya taya wadanda suka yi rashin nasara a zabukan fitar da gwani murna, yana mai nuna fatan cewa za a samu mafita ga wasu daga cikinsu.

Ya bayyana cewa shugabannin majalisar sun yi mamakin yawan sanatocin da suka rasa damar sake tsayawa takara:

“Ina taya musamman wadanda suka samu tikitin jam’iyyunsu domin wakiltarsu a zabe mai zuwa murna. Na san cewa a siyasa akwai nasara da rashin nasara.”
“Kuma a wannan majalisar dattawa, mun yi alkawarin cewa za a samu ‘yan kadan ne kawai da za su fuskanci matsala, kuma na san shugaban majalisa da sauran shugabanni suna aiki tukuru wajen ganin hakan ya tabbata.
"Saboda haka tun daga yanzu ina cewa taya murna gare mu baki daya ba tare da la’akari da jam’iyya ba,”

Daga cikin sanatocin da suka rasa tikitin komawa takara akwai Sanata Ned Nwoko, Sanata Gbenga Daniel, Sanata Danjuma Goje da Sanata Rufai Hanga.

Kara karanta wannan

Galadima: Mutum 1 da ya samu takara a APC cikin mukarraban Tinubu 7 da suka yi murabus

Goodswill Akpabio na tafiya a majalisa
Sanatoci bayan tashi daga zama a majalisa. Hoto: Nigerian Senate
Source: Twitter

Magana kan daliban Oyo

Akpabio ya kuma nuna damuwarsa kan sace dalibai da malamai a Jihar Oyo, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa domin ganin an kubutar da su.

Premium Times ta wallafa cewa ya gargadi ‘yan siyasa da masu neman mukamai da kada su rika amfani da irin wadannan masifu domin samun wata riba ta siyasa.

“A irin wadannan lokuta, akwai yiwuwar a fara rarrabuwa kawuna da jefa zargi. Ya kamata ‘yan siyasa da masu neman mukamai su guji hakan, domin irin wannan neman suna ba shi da amfani.”

Sanata Nwoko ya yi korafi

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Ned Nwoko daga jihar Delta ya yi korafi kan zaben fitar da gwani da aka yi ya sha kaye.

Sanata Nwoko ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta masa alkawarin tikitin takara a alokacin Abdullahi Umar Ganduje kafin ya koma cikinta.

Ya kuma yi ikirarin cewa shi ya ci zaben, inda ya kalubalanci wakilan jam'iyyar da su fitar da biyon yadda aka kirga kuri'u a dukkan mazabun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng