Tsagin PDP na cikin Barazanar Rasa Jonathan a matsayin 'Dan takarar Shugaban kasa

Tsagin PDP na cikin Barazanar Rasa Jonathan a matsayin 'Dan takarar Shugaban kasa

  • Makusantan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan sun warware batun shirin da ake yi na tsaida shi takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027
  • Sun ce babu wata alama da ke nuna Jonathan na neman komawa takara, tare da zargin wasu na amfani da sunansa domin cimma muradunsu na siyasa
  • Sai dai wani ɓangaren PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya dage cewa Jonathan ne ɗan takararsu na shugaban ƙasa a 2027 tare da bayyana dalilinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wasu na kusa da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, sun yi watsi da jita-jitar da ke cewa yana shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Majiyoyin, waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu saboda ba su da izinin yin magana a hukumance, sun bayyana cewa babu wata shaida ko alamar da ke nuna tsohon shugaban na son komawa takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

'Tinubu jan wuya ne a murde zabe': Babachir Lawal na ganin APC za ta zarce

Ana ganin Jonathan ba zai yi takara a 2027 ba
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa makusantan tsohon shugaban sun ce rahotannin da ke alaƙanta Jonathan da takarar 2027 na da nasaba da wasu manufofin siyasa.

Matsayar Goodluck Jonathan kan takarar 2027

Makusantan Jonathan sun kara da bayyana cewa nan gaba kaɗan za a fitar da sanarwa domin fayyace matsayinsa kan lamarin duk da cewa tsagin PDP ya riga ya ba shi takara.

Tun bayan fara shirye-shiryen zaɓen 2027, wani ɓangaren jam'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya riƙa ikirarin cewa Jonathan ya yi rajista da shi, har ma ya sayi fam ɗin nuna sha'awa da na tsayawa takara.

Sai dai majiyoyin sun ce babu wata hujja da aka gabatar da ke tabbatar da waɗannan ikirari, hasali ma bai ce komai a kan batun ba zuwa yanzu a cewar Daily Post.

Jonathan ya yi gum kan batun takara

A cewar wata majiya, da Jonathan yana da niyyar tsayawa takara, da tuni ya yi zaman tuntuba da gina tsarin siyasa a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Yadda Iran ta haddasa asarar biliyoyin Daloli, ta lalata sansanonin Amurka 20

Ya ce:

"Mu da ke kusa da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan mun san cewa ba ya takarar zaɓen 2027."

A cewarsa, wasu mutane ne kawai ke amfani da sunan Jonathan domin ciyar da muradunsu gaba da kuma ƙarfafa ɓangarensu na siyasa.

PDP tsagun Tanimu Turaki ta nace cewa Jonathan zai yi mata takara
Shugaban riko na tsagin jam'iyyar PDP Tanimu Turaki Hoto: Tanimu Turaki
Source: Twitter

Duk da waɗannan bayanai, sakataren yaɗa labarai na kwamitin riƙon ƙwarya na PDP ƙarƙashin Tanimu Turaki, Ini Ememobong, ya dage cewa Jonathan na cikin masu neman shugabancin ƙasa.

Ya ce shirun da tsohon shugaban ke yi wani salo ne na siyasa, yana mai cewa ba kowane ɗan siyasa ne ke bayyana manufofinsa a fili tun da wuri ba.

A cewarsa:

"Shiru ma wata dabara ce kamar yadda magana dabara ce."

Kano: PDP ta goyi bayan Jonathan

A wani labarin, kun ji cewa PDP reshen jihar Kano ta cimma matsayar a kan mara wa dan takarar shugaban kasa da tsagin Tanimu Turaki ya fitar yayin da rikici ya dabaibaye jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala Muhammad ya yi bayani game da hada takara da Jonathan a PDP

Shugaban PDP na Kano, Yusuf Ado Kibiya, ya ce jam'iyyar ta amince da matakin da shugabancin ƙasa ya ɗauka bisa tanadin kundin tsarin mulki kuma za a ci gaba da hada kai.

Jam'iyyar PDP na da 'yan takarar shugaban kasa guda biyu - tsohon shugaba Goodluck Jonathan na tsagin Turaki da Sandy Onor na tsagin Nyesom Wike yayin da ake fama da rikicin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng