ICPC ta Miƙa Wa Tinubu Rahoton Abubuwan da Ta Gano kan Badakalar Kafa Hukumar Bogi
- Hukumar ICPC ta mika wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu rahoton wucin gadi kan binciken PFIPC ta ake ta magana a kanta
- Hukumar ta ce Prince Adeyemi Matthew bai taba samun nadi daga gwamnatin tarayya a hukumance ba
- Ta bayyana cewa PFIPC ba ta da tushe a doka ko umarnin zartarwa, yayin da takardun nadin da aka yi anfani da su duk na jabun ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Yaki da Rashawa (ICPC) ta kammala bincike kan hukimar Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) da aka ce ta bogi ce.
Bayan kammala bincike, hukumar ICPC ta tabbatar da cewa ta mika rahoton wucin gadi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Twitter
Shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan mika rahoton, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Ya ce binciken ya tabbatar da cewa Prince Adeniyi Adeyemi Matthew, wanda ke ikirarin shi ne shugaban hukumar bogi, bai taba samun nadi daga fadar shugaban kasa ko wata hukuma ta gwamnatin tarayya ba.
PFIPC ba ta da tushe a doka
Bayan ce-ce-ku-cen da suka dabaibaye wannan hukuma, Shugaba Tinubu ya umarci ICPC a ranar 7 ga Yuli da ta gudanar da bincike tare da gabatar da rahotonta cikin kwanaki 30.
Shugaban ICPC ya ce binciken ya gano cewa:
"An tabbatar cewa Adeyemi Matthew bai taba samun nadi daga gwamnatin tarayya ko wata hukuma ta gwamnati ba."
A cewarsa, takardar nadin da Adeyemi ya gabatar ta jabu ce, haka ma sauran takardun da aka yi anfani da su wajen gudanar da ayyukan wannan haramtacciyar hukuma.
Ya kwace tsohon ofishin gwamnati
Shugaban ICPC ya bayyana cewa Adeyemi ya yi anfani da tsohon ofishinnPresidential Economic Advisory Council wajen kirkirar wannan hukuma ta bogi, sannan ya kwace ofishinta ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan
Malamin addini ya tubure kan dokar gwamnatin Tinubu na hana wa'azi, ya sha alwashi
A rahoton Vanguard, ya ce:
"Mun gano cewa an balle makullin ofishin, sannan ya shiga ciki ya mamaye wurin. Daga nan ne ya fara gudanar da ayyukan wannan hukuma ta bogi da kuma yaudarar jama'a."
Ya kuma ce binciken ya nuna akwai gibin tsarin tantancewa da sa ido tsakanin hukumomin gwamnati, lamarin da Adeyemi ya yi anfani da shi saboda sakacin wasu jami'an gwamnati.

Source: Facebook
ICPC ta ba da shawarwari
Hukumar ICPC ta ba da shawarar gurfanar da Adeyemi Matthew a gaban kotu bisa laifukan da ake zarginsa da su.
Ta kuma bukaci a hukunta jami'an gwamnati da bincike ya nuna sakacinsu ya taimaka wajen bai wa wannan hukuma ta bogi damar gudanar da ayyukanta.
ICPC ta kuma ba da shawarar a sake fasalin tsarin kula da hukumomin gwamnati domin karfafa hanyoyin sa ido da hana irin wannan lamari sake faruwa a nan gaba.
PFIPC: Yadda aka damfari dan kasuwa N400m
A wani labarin, kun ji cewa wani dan kasuwa, Gbenga Collins ya ce ya ba Adeniyi Adeyemi N400m domin a saukaka ba kamfaninsa kwangilar gyara da samar da kayan daki.
Collins ya ce ya dauki PFIPC a matsayin halastacciyar hukumar gwamnatin tarayya saboda Adeyemi na aiki daga wani ofishi da ke sakatariyar tarayya a Abuja .
Asali: Legit.ng
