Dan Majalisar PDP Ya San Makomarsa da Aka Kai Shi gaban Kotu bayan Barin APC
- Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan karar PDP da ke neman a kwace kujerar ɗan majalisar Benue, Anthony Attah, bayan ya koma APC
- Kotun ta ce kundin tsarin mulki ya bai wa kakakin majalisar Benue da majalisar ikon ayyana kujerar babu kowa, ba kotu ba
- Alkalin ya ce INEC ba za ta iya shirya zaben cike gurbi ba sai bayan majalisar ta ayyana kujerar babu kowa sannan kakaki ya sanar da hukumar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi zama game da karar da PDP ta shigar kan wani ɗan majalisa a Benue.
Kotun ta yi watsi da karar da jam'iyyar PDP ta shigar tana neman a tsige ɗan majalisar dokokin Benue mai wakiltar mazabar Okpokwu, Anthony Attah, bayan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Source: Original
A hukuncin da Alkalin kotun, Muhammed Umar, ya yanke ranar Talata kan shari'a mai lamba FHC/ABJ/CS/2408/2025, cewar TheCable.
Kotun ta tsame kanta daga korafin PDP
Ya ce ko da yake Attah bai musanta sauya shekarsa daga PDP zuwa APC ba, kotun ba ta da ikon kundin tsarin mulki na ayyana kujerarsa a matsayin wacce babu mai ita.
Alkalin ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa majalisar dokokin Benue da kakakinta wannan iko, don haka kotu ba za ta iya karɓe musu wannan hakki ba.
Ya ce, sanar da cewa ɗan majalisar ya sauya sheka daga PDP zuwa APC kaɗai bai isa a kwace kujerarsa ba.

Source: Facebook
Hujjar da alkalin kotun ya bayar
Alkalin ya yi nuni da sashe na 109 na kundin tsarin mulkin 1999, inda ya ce dole ne majalisar dokokin Benue ta fara ayyana kujerar babu kowa kafin kakakin majalisar ya sanar da hukumar INEC domin shirya zaben cike gurbi.

Kara karanta wannan
Majalisar shari'ar musulunci ta Najeriya ta hango matsala a shirin kafa yan sandan jihohi
Ya ƙara da cewa har sai an bi wannan tsari, INEC ba za ta iya ɗaukar wani mataki ba, cewar Daily Post.
Alkalin ya jaddada cewa kotu ba za ta kwace ikon da kundin tsarin mulki ya bai wa kakakin majalisa da 'yan majalisar ba.
A cikin karar, PDP ta shigar da INEC da APC da kuma Anthony Attah kara, tana neman kotu ta fayyace ko kuri'un da aka kada wa wata jam'iyya za su iya komawa wata jam'iyya bayan ɗan majalisa ya sauya sheka.
Jam'iyyar ta kuma nemi kotu ta ayyana cewa ci gaba da zaman Attah a majalisar bayan barin PDP ya saba wa doka, tare da soke duk matakan majalisa da ya shiga bayan sauya shekar.
Har ila yau, PDP ta bukaci kotu ta umurci Attah ya mayar da duk albashi, alawus da sauran hakkokin da ya karɓa tun bayan komawarsa APC.
A hukuncinsa, Alkalin Umar ya ce Attah bai musanta cewa ya sauya sheka zuwa APC ba, amma hakan kaɗai bai isa kotu ta ɗauki matakin da PDP ke nema ba.
Jiga-jigan PDP sun koma APC a Gombe
Mun ba ku labarin cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP guda biyu a jihar Gombe sun yi murabus daga jam’iyyar yayin da ake shirin zaben 2027.
Tsohon shugaban karamar hukumar Funakaye, Ibrahim Yusuf, ya ce ya janye kansa daga PDP nan take.
Mataimakin sakataren PDP a jihar Gombe, Mohammed Babani Bajoga, shi ma ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.
Asali: Legit.ng

