Yadda Iran ta Haddasa Asarar Biliyoyin Daloli, Ta Lalata Sansanonin Amurka 20
- Wani rahoton kwa-kwaf ta bayyana cewa hare-haren Iran sun lalata ko kuma sun yi wa sansanonin sojin Amurka 20 ɓarna a ƙasashe takwas na Gabas ta Tsakiya
- Hotunan tauraron ɗan’adam sun nuna cewa ɓarnar ta fi yadda jami’an Amurka suka bayyana a baya, inda suke nuna ba a yi masu wata illa ta a zo a gani ba
- Masana sun yi gargaɗin cewa wasu muhimman kayan yaƙin Amurka da aka lalata ba su da sauƙin da za a maye gurbinsu a cikin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar America - Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa Iran ta haddasa gagarumar ɓarna ga aƙalla sansanonin sojin Amurka 20 a Gabas ta Tsakiya tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin ɓangarorin biyu.
Rahoton ya ce Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin soji da ke ƙasashe takwas, daga ciki har da Saudiyya, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Qatar, Kuwait, Iraqi, Jordan, Bahrain da Oman.

Source: Getty Images
Binciken kwakwaf da BBC Hausa ya nuna cewa hare-haren sun lalata na’urorin tsaron sararin samaniya, na’urorin kakkaɓo makamai masu linzami da kuma wasu muhimman jiragen yaƙin Amurka.
Iran ta kai wa Amurka munanan hare-hare
A cewar rahoton, Tehran ta fara kai hare-haren ne domin mayar da martani ga hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a cikin Iran da Lebanon.
Sai dai Fadar White House ta ci gaba da jaddada cewa sojojin Iran sun tafka mummunar asara a yaƙin da aka shafe watanni biyar ana gwabza wa.

Source: Facebook
Masana da suka yi nazarin hotunan tauraron ɗan’adam sun ce adadin sansanonin da aka kai wa hari na iya kai wa 28, duk da cewa an tabbatar da aƙalla 20 da suka samu ɓarna kai tsaye.
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi ikirarin cewa hare-haren sun nuna cewa sansanonin Amurka ba su da cikakken tsaro a yankin.
Ya kuma ce Gabas ta Tsakiya ba za ta ci gaba da kasancewa wurin da Amurka ke gudanar da ayyukan soja cikin kwanciyar hankali ba.
Muhimman kayan yaƙi da Iran ta lalata
Daga cikin manyan abubuwan da aka lalata akwai na’urorin kariya daga makamai masu linzami na THAAD guda uku da ke wasu sansanonin Amurka a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Jordan.
Rahoton ya bayyana cewa Amurka tana da irin waɗannan na’urori kaɗan a duniya, kuma kowace na da matuƙar tsada. Masana tsaro sun ce maye gurbinsu cikin gaggawa abu ne mai wahala.
Haka kuma, hare-haren sun yi illa ga jirgin zuba wa jiragen yaƙi mai a sama da kuma jirgin sintirin sa ido ƙirar E-3 a Sansanin Yarima Sultan da ke Saudiyya. An ce irin wannan jirgi yana da darajar fiye da Dala miliyan 700.
Binciken ya gano cewa aƙalla jiragen sama 42, daga ciki har da jiragen yaƙi ƙirar F-15 da F-35 da kuma jirage marasa matuƙi na MQ-9 Reaper, sun lalace ko suka samu matsala tun bayan fara yaƙin.
Pentagon ya ƙiyasta cewa kuɗin gyare-gyare da maye gurbin kayan da aka lalata ya kai kusan dala biliyan 29. Sai dai wasu ‘yan siyasar Amurka sun ce ainihin asarar na iya zarce wannan adadi.
An ba Netanyahu shawara game da Amurka
A baya, mun wallafa cewa wani minista mai tsattsauran ra'ayi a Isra'ila ya bukaci Firaminista Benjamin Netanyahu ya fara yi wa Amurka da bukatunta bore kan hare-haren da ta ke kai wa Lebanon.
Iran dai ta kafe a kan cewa babu maganar sulhu matukar Isra'ila ba ta daina kai harin ta'addanci wasu sassan Lebanon da ake ganin tana neman mamaye wa ba ta hanyar kashe bayin Allah a wurin.
Ministan Tsaron Cikin Gida na Isra’ila, Itamar Ben-Gvir,ya bayyana cewa ya kamata Isra'ila ta daina daukar shawarar wata kasa a kan al'amuranta na tsaro, musamman yaki da Hezbollah.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


