'Tinubu Jan Wuya ne a Murde Zabe': Babachir Lawal na Ganin APC za Ta Zarce

'Tinubu Jan Wuya ne a Murde Zabe': Babachir Lawal na Ganin APC za Ta Zarce

  • Tsohon sakataren gwamnati, Babachir Lawal ya yi zargin cewa zai yi wuya a kayar da Bola Tinubu a 2027 idan maguɗin zaɓe ne ke tabbatar da nasara
  • Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyan ya ce Tinubu zai fi kowane ɗan takara iya murɗe sakamakon zaɓe jim kadan bayan ya sanar da ficewa daga jam'iyyar ADC
  • Ya kuma soki Atiku Abubakar tare da bayyana dalilin da ya sa yake kiransa da lakabin “Kachalla” yayin da ya raba gari da tafiyarsu gabanin zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya yi ikirarin cewa akwai alamun Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zarce.

Ya kara da cewa zai yi matuƙar wahala a kifar da APC a zaben shugaban kasa na 2027 idan har abin da ke tabbatar da nasara shi ne maguɗin zaɓe.

Kara karanta wannan

'Atiku da Peter Obi su sake bude wa Tinubu kofa, APC na iya lashe zaben 2027'

Babachir Lawal ya soki Tinubu
Babachir Lawal da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Babachir Lawal, @OfficialABAT
Source: Twitter

Babachir Lawal ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 1 ga watan Mayu, 2026 yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Television.

Babachir Lawal ya magantu kan Bola Tinubu

The Cable ta wallafa cewa da aka tambaye shi ko yana ganin Tinubu ya riga ya tabbatar da nasara a zaɓen 2027. Da yake amsa tambayar, Babachir ya yi zargin cewa shugaban ƙasar zai yi amfani da dabarun murɗe zaɓe wajen rinjayar sauran ’yan takara.

Ya ce:

“Da gagarumar rinjaye. Zai fi kowa iya murɗe zaɓe.”

Ya ƙara da cewa:

“Idan ma’aunin cin zaɓe a Najeriya shi ne maguɗi, babu wanda zai iya tunkarar Bola Tinubu a wannan fanni.”

Babachir Lawal ya caccaki Atiku Abubakar

A wata magana da ya yi yayin hirar, Babachir ya soki Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, inda ya yi zargin cewa shi ma ya iya murde zabe.

Kara karanta wannan

2027: Babachir Lawal ya rikita lissafin Atiku Abubakar, ya fice daga jam'iyyar ADC

Lokacin da aka tambaye shi ko yana danganta Atiku da jagororin ’yan bindiga ko masu ta’addanci, Babachir ya ce kalmar tana da alaƙa da yadda wasu Fulani ke kiran shugabanninsu.

Babachir Lawal ya yi zargin Atiku Abubakar ma yana murde zabe
Tsohon sakataren gwamnati a Najeriya, Babachir Lawal Hoto: Babachir Lawal
Source: Twitter

Ya ce:

“Mutanensa a cikin daji suna kiran shugabanninsu da Kachalla. Shin ba Bafullatani ba ne?”

Babachir ya kuma yi tambaya kan yadda wasu Fulani suka nuna farin ciki bayan Atiku ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC.

Ya ce suna murnar cewa ɗan uwansu ne ya samu tikitin takara, sannan ya yi zargin cewa bai taɓa jin Atiku ya fito fili yana Allah wadai da sace-sacen mutane da kashe-kashen da ake yi a wasu sassan ƙasar nan ba.

Kungiya ta fito ta soki Babachir Lawal

A baya, mun wallafa cewa kungiyar matasan APC, reshen Arewa maso Gabas (APC-YPNE) ta caccaki tsohon sakataren gwamnatin kasar nan, Babachir Lawal saboda kalamansa kan Kashim Shettima.

Shugaban kungiyar, Kabiru Garba Kobi ya zargi Babachir da raina Shettima tare da nuna kiyayyarsa a fili kan tikitin Muslimi da Muslmi na 2023 da jam'iyyar APC ta tsayar har ta kai ga samun nasararsu.

Kabiru Garba Kobi ya ce hassada ce kawai ke cin Babachir, kuma yana ji yana gani mataimakin shugaban kasar, Shettima zai kara daukaka a gwamnatin APC tare da samun karbuwa a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng