Gwamna Bala Mohammed Ya Yi Bayani game da Hada Takara da Jonathan a PDP

Gwamna Bala Mohammed Ya Yi Bayani game da Hada Takara da Jonathan a PDP

  • Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa zai yi takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Goodluck Jonathan a 2027
  • Wannan na zuwa ne a loakcin da ya ke neman kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APM da ya koma bayan ya fice daga jam'iyyar PDP
  • Tsagin jam'iyyar ya sanar da tsaida Goddluck Jonathan takarar shugaban kasa duk da rikicin da ya dabaibaye su bayan Nyesom Wike ya ja daga game da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya fito ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa yana cikin shirye-shiryen tsayawa takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

'Idan na zama shugaban ƙasa,' Makinde ya fadi ayyukan da zai yi wa Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin magoya bayan tsagin jam’iyyar PDP sun fara yaɗa bayanan cewa ana tunanin haɗa Jonathan da Bala Mohammed a matsayin tikitin shugaban ƙasa da mataimakinsa domin fafatawa a zaɓen mai zuwa.

Bala Mohammed ya magantu kan takara da Jonathan
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan tare da Gwamna Bala Mohammed Hoto: @NuhuSada0
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan jita-jita ta ƙara ɗaukar hankali ne bayan tsagin PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki ta ayyana Jonathan a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a wani babban taron ƙasa da aka gudanar a Abuja ranar Asabar.

Bala Mohammed ya yi martani kan takara

Da yake mayar da martani ta shafinsa na X, Gwamna Bala Mohammed ya ce babu kamshin gaskiya a rahotannin da ake yaɗawa dangane da wata takarar shugaban ƙasa ko mataimakinsa.

Gwamnan ya bayyana cewa manufarsa a yanzu ita ce neman wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawa ƙarƙashin tutar jam’iyyar APM.

Gwamna Bala Mohammed ya ce hankalinsa yana kan takarar Sanata
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed a wani taro Hoto: Senator AbdulKadir Bala Mohammed
Source: Twitter

Ya rubuta cewa:

“Na gode da irin kulawar da ku ke nunawa game da burina na siyasa. Amma gaskiya ita ce, hankalina da burina suna nan daram kan neman kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a ƙarƙashin jam’iyyar APM.”

Kiran Bala Mohammed ga magoya baya

Kara karanta wannan

Martanin Kwankwaso bayan samu tikitin takarar mataimakin Peter Obi a NDC

Gwamna Bala Mohammed ya kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da duk wasu rahotannin da ke nuna yana shirin shiga wata takarar daban.

A cewarsa, duk wani bayani da ke nuna yana da wata manufa ta siyasa da ba wannan ba, hasashe ne kawai kuma ba ya da tushe.

Jita-jitar ta ja hankali ne musamman ganin gwamna Bala Mohammed ya riga ya bar PDP, shi kuma Jonathan ya samu takara ne a tsagin jam'iyyar da ke fama da rikice-rikice da Nyesom Wike, Ministan babban birnin tarayyya Abuja.

Gwamna Bala Mohammed ya tsayar da dan takara

A baya, mun wallafa cewa Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya sha alwashin tunkarar duk wani nau’i na magudin zabe a babban zaben 2027 domin sun shirya tabbatar da adalci.

Bala Mohammed ya yi magana ne yayin da jam’iyyar APM ta tabbatar da shi a matsayin dan takararta na Sanata a mazabar Bauchi ta Kudu inda shi kuma ya kaddamar da wanda zai yi masu takarar gwamna.

Jam'iyyar ta APM ta kuma ta tabbatar da kwamishinan kudi, Yakubu Adamu, a matsayin dan takararta na gwamna da Nuhu Zaki a matsayin dan takarar Sanata a cikin shirye-shiryen gudanar da babban zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng