Bayan Sukar Kalamansa a 2023, Peter Obi Ya Shawarci Matasa kan Siyasar Addini, Kabilanci

Bayan Sukar Kalamansa a 2023, Peter Obi Ya Shawarci Matasa kan Siyasar Addini, Kabilanci

  • Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya shawarci matasan Najeriya yayin da ake tunkarar zaben 2027
  • Obi ya buƙaci matasan Najeriya su guji rarrabuwar kawuna ta hanyar ƙabilanci da addini, su rungumi haɗin kai
  • Tsohon gwamnan ya ce bayan zaɓen 2023 a Lagos, tattaunawa ta karkata zuwa ƙabilanci wanda bai dace ba ko kadan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi ya ba da shawara game da siyasar Najeriya.

Peter Obi ya buƙaci matasan Najeriya da su yi watsi da rarrabuwar kawuna ta ƙabilanci da addini, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai da makomar ƙasa.

Peter Obi ya nuna damuwa kan siyasar kabilanci da addini
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: UGC

A cikin saƙon da ya wallafa a shafin X, Obi ya yi nazari kan darussan da aka koya daga zaɓen shekarar 2023, musamman a Lagos.

Kara karanta wannan

Lokuta 3 da Babachir Lawal ya canza gidan siyasa daga mulkin Buhari zuwa yau

Gargadin da Peter Obi ya yi kan siyasa

Ya ce tattaunawar jama'a ta kauce daga batutuwan shugabanci da ci gaba zuwa na ƙabila da bambance-bambancen kabilanci.

Ya gargadi cewa irin waɗannan bayanai suna sake bayyana, tare da kira ga ‘yan Najeriya su kasance cikin shiri.

Obi ya ce wasu ‘yan siyasa kan koma amfani da ƙabila, addini da batutuwan asali idan ba za su iya yin gogayya ta fuskar tunani, aiki, hali ko hangen nesa ba.

Ya bayyana cewa mutane da dama na shiga irin waɗannan muhawarori ba tare da sanin cewa ana jan su cikin labaran da wasu suka ƙirƙira ba.

Ya ƙara da cewa wasu kamfen-kamfen na samun yaɗuwa ne ta hannun mutanen da ke tunanin suna goyon bayan kyakkyawan manufa alhali ba su fahimci wata babbar manufa da ke bayan hakan ba.

Obi ya ba matasa shawara game da zaɓen 2027
Tsohon gwamnan Anambra kuma mai neman takarar shugaban ƙasa a NDC, Peter Obi. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Twitter

Obi ya yabawa babban fasto a Najeriya

Tsohon gwamnan Anambra ya kuma yi magana kan babban mai kula da cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye.

Kara karanta wannan

Yadda Iran ta haddasa asarar biliyoyin Daloli, ta lalata sansanonin Amurka 20

Ya bayyana Adeboye a matsayin ɗaya daga cikin manyan shugabannin Kiristoci na Najeriya wanda ya dade yana wa’azin zaman lafiya, addu’a, soyayya, sulhu da haɗin kai na ƙasa.

Peter Obi ya ce bai dace matasa su ɗora wa Fasto Adeboye mai shekaru 84 nauyin da ya rataya a wuyansu ba, ya ce babban nauyin gina Najeriya mafi kyau yana kan matasa.

Ya rubuta cewa:

“Aikin gina Najeriya mafi kyau ya rataya ne a wuyan matasa. Su ne ya kamata su jagoranci tattaunawa, su ɗauki nauyin gyare-gyare, kuma su jagoranci canjin da ƙasarmu ke matuƙar buƙata.”

Ya kuma gargadi ‘yan Najeriya da kada su zama kayan aiki a hannun masu yaɗa rarrabuwar kawuna yayin da a fili suke kiran haɗin kai.

An kwatanta tsarin siyasar Obi da ta Buhari

Mun ba ku labarin cewa masani kan harkokin siyasa ya bayyana cewa matsalolin Najeriya sun fi karfin mutum guda ɗaya duba da matsalar kasar.

Masanin harkokin siyasar nan, Sola Kuti ya bayyana cewa tsarin siyasa ne babban kalubalen da ke hana ci gaba a Najeriya.

Ya ce ko shugaba mai kyakkyawar niyya zai fuskanci cikas daga masu ruwa da tsaki da tsarin da ke hana sauye-sauye masu ma'ana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.