'Matsin Lambar Siyasa,' INEC Ta Dauki Mataki da Aka Nemi Ta Soke Rajistar ADC
- Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana ƙwaƙƙwarar adawarta ga yunƙurin soke rajistar jam'iyyar adawa ta ADC a gaban kotu
- Hukumar ta kafa hujjar cewa wannan buƙata ba ta cika sharuɗɗan kundin tsarin mulki ba, kuma soke rajistar jam'iyya dole ne ya bi tsarin doka
- Wannan takaddama na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar ke fama da rikicin shugabanci da kuma ficewar manyan mambobi kamar Rabiu Kwankwaso
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta nuna adawa ga wani yunƙuri na soke rajistar jam'iyyar adawa ta ADC.
Ƙungiyar tsofaffin ƴan majalisu ta kasa ce ta nemi umarnin kotu domin soke rajistar jam'iyyar adawar, kamar yadda Legit Hausa ta ruwiato.

Source: Twitter
INEC ta bijire wa bukatar soke rajistar ADC

Kara karanta wannan
NDC: Kwankwaso ya mika sakon kar ta kwana gabanin rufe rajistar jam'iyyu a Najeriya
A cikin takardun kotu da jaridar The Cable ta gani, hukumar zaɓen ta bayyana cewa buƙatar mai ƙarar ta gaza cika muhimman sharuɗɗan kundin tsarin mulki.
INEC ta ce soke rajistar kowace jam'iyyar siyasa yana ƙarƙashin jagorancin dokoki ne da tanadin kundin tsarin mulki, kuma matsin lambar siyasa ba zai sa a aiwatar da shi ba.
Hukumar ta jaddada cewa ba a gabatar da dalili ko ɗaya ba daga cikin dalilan soke rajistar jam'iyya da kundin tsarin mulki ya amince da su.
Daga cikin ire-iren wadannan dalilai akwai gazawar samun nasara a zaɓukan shugabanni ko keta sharuɗɗan rajista.
Takaddamar shugabanci a jam'iyyar ADC
A ranar 30 ga watan Afrilu, Kotun Ƙoli ta umarci David Mark, shugaban wani ɓangare na jam'iyyar ADC, da Nafiu Bala, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa, da su koma Babbar Kotun Tarayya domin sauraro da kuma yanke shawara kan al'amuran da suka shafi takaddamar shugabanci a cikin jam'iyyar.
Tun bayan wannan hukuncin, jam'iyyar ta fuskanci ficewar mambobi da dama, inda Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, suka sauya sheka zuwa jam'iyyar NDC, in ji rahoton Legit Hausa.

Source: Twitter
Martanin hadimin Atiku kan matakin INEC
Yayin da yake mayar da martani kan wannan lamari, Phrank Shaibu, Babban Mataimaki na Musamman ga tsohon Atiku Abubakar, ya bayyana yunƙurin soke ADC a matsayin wani shiri na siyasa kawai, in ji rahoton Punch.
"Ganin cewa ita kanta INEC ta fito domin ruguza tushen shari'ar wannan buƙatar, hakan ya nuna abubuwa da dama. Ya tabbatar da abin da ƴan Najeriya suka riga suka yi zargi, cewa wannan ba batun shari'a ba ne, batun tursasawa hukuma ne ta yi abin da ya saba wa doka," in ji Phrank Shaibu.
Shaibu ya yi gargaɗi game da abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarin raunata adawa a siyasar Najeriya.
ADC ta sauya tsarin zaben fitar da gwani
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ADC ta fitar da sabon jadawalin ayyukan zaɓukan fitar da gwani na shekarar 2026, inda ta bayyana ranakun sayar da fom da na zabe.
Sanarwar ta nuna cewa jam'iyyar ta sauya farashin fom ɗin takarar shugaban ƙasa, gwamnoni, da na 'yan majalisar tarayya da majalisun jihohi.
Duk da haka, jam'iyyar ta ci gaba da bayar da rangwamen kashi 50 ga matasa, da kuma rangwamen kashi 25 ga mata da masu bukata ta musamman.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

