An Kama Malamin Addini da Mahaifiyar Yarinya kan 'Kisan' Ƴarta da Dukan Tsiya
- 'Yan sanda sun kama wata mata da malamin addinin Kirista bayan mutuwar diyarta, Nancy Peter mai shekaru 14 a Boki
- Binciken farko ya nuna cewa mahaifiyar yarinyar ta doke ta kan zargin sata, sannan ta kai ta wurin fasto wanda shi ma ya yi mata bulala
- Bayan dukan da aka yi mata, Nancy ta suma kuma aka garzaya da ita asibiti a Wula, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Calabar, Cross River - Rundunar ‘yan sandan Najeriya a Cross River ta fara bincike kan mutuwar wata yarinya mai shekaru 14 mai suna Nancy Peter.
Ana zargin yarinyar ta mutu bayan dukan da mahaifiyarta da wani fasto suka yi mata a karamar hukumar Boki.

Source: Original
‘Yan sanda sun cafke mahaifiyar marigayiya
‘Yan sanda sun bayyana cewa mahaifiyar yarinyar, Agnes Peter mai shekaru 45, da Fasto Samson Dago mai shekaru 43 suna tsare a hannunsu dangane da lamarin da ya faru a yankin Wula, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kai mummunan hari masallaci ana tsakiyar sallar Magriba a Kaduna
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, Eitokpah Sunday, ya fitar, ya ce binciken farko ya nuna cewa an zargi yarinyar da sata.
Jami’in ya ce ana zargin mahaifiyar Nancy ta fara dukanta saboda zargin sata, kafin daga bisani ta kai ta wurin faston domin ya yi mata horo.
Sanarwar ta ce bayan kai yarinyar wurin faston, shi ma ya yi mata bulala da dorina a matsayin hukunci, lamarin da ya kara tsananta halin da take ciki.
Ta ce:
“Binciken farko ya nuna cewa an yi wa yarinyar duka bisa zargin sata. Haka kuma an kai ta wurin Fasto Samson Roman Dago wanda shi ma ake zargin ya yi mata bulala."
‘Yan sanda sun ce daga baya Nancy ta suma sakamakon abin da ya faru, kuma aka garzaya da ita wani asibiti da ke Wula domin samun kulawar likitoci.
Sai dai jami’an lafiya da suka karbe ta a asibitin sun tabbatar da cewa yarinyar ta rasu bayan an kawo ta wurin jinya.

Source: Twitter
Ƴan sanda sun ƙaryata maganar cin zarafinta
Rundunar ‘yan sanda ta kuma yi magana kan rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa an ci zarafin yarinyar kafin mutuwarta.

Kara karanta wannan
"Kun tona wa kanku asiri," Wike ya taso Atiku, Peter Obi da Kwankwaso ana shirin zaben 2027
Kakakin rundunar ya ce zuwa yanzu masu bincike ba su samu wata hujja da ke tabbatar da wannan zargi ba, duk da cewa bincike yana ci gaba, cewar Daily Post.
Ya ce rundunar ta fara cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya jawo mutuwar yarinyar tare da tantance rawar da kowane mutum ya taka.
Ya kara da cewa za a dauki matakin shari’a da ya dace da duk wanda aka samu da hannu a lamarin bayan kammala binciken.
Lamarin ya sake tayar da hankalin jama'a kan matsalar cin zarafin yara da amfani da hukuncin duka a Najeriya duk da dokokin da ke kare hakkokin yara.
An kama dattijo yana safarar makamai
Mun ba ku labarin cewa rundunar 'yan sanda ta cigaba da kara kaimi wajen yaki da safarar makamai a Najeriya a kokarin yaki da 'ya ta'adda masu kai hari a yankuna.
Rahotanni sun nuna cewa an kama wani tsoho dan shekara 60 da ake zargi yana safarar makamai da ake amfani da su ba bisa ka'ida ba.
Kakakin 'yan sandan jihar Cross River, Sunday Eitokpah ya yi karin haske kan kama tsohon da matakan da hukumomi za su dauka a kansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng