"Kwankwasiyya Murhu Ce": NDC Ta Yi Martani da Hanga Ya Rabu da Jam'iyya
- Jam'iyyar NDC a Kano ta fitar da sanarwa jim kadan bayan an fitar da sanarwar cewa Sanata Rufa'i Hanga ya fice daga cikinta da tsarin Kwankwasiyya
- Duk da har yanzu Sanata Rufa'i Hanga bai sanar da jam'iyyar da zai koma ba, amma an ga yadda manyan APC suka rika kai masa ziyara
- Kakakin jam'iyyar NDC, Yusuf Rabi'u Fasaha, ya ce wani lokaci rabuwa da ɗan siyasa na iya zama alheri idan aka gano illar da ke tattare da zamansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Mai magana da yawun jam'iyyar, Yusuf Rabi'u Fasaha, ne ya bayyana haka bayan Sanata Rufa'i Hanga da tsohon gwamnan jihar Kano, Kabiru Gaya, sun fice daga jam'iyyar NDC a ranar Litinin, 3 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare: Sanata Hanga ya bar tafiyar Kwankwaso, ya fice daga jam'iyyar NDC
Wannan na zuwa ne bayan Sanata Hanga ya jima yana tattaunawa da yan siyasa musamman 'yan APC kan batun sauya sheka.

Source: Facebook
A wata hira da ya yi da Daily Nigerian, wadda aka wallafa a shafinta na Facebook, Fasaha ya ce a wasu lokuta rabuwa da ɗan siyasa na iya zama alheri.
NDC ya yi martani ga Hanga
Ya ƙara da cewa maimakon ci gaba da zama tare da ɗan siyasar da ba zai kasance mai aminci ba, ya fi dacewa a rabu da shi domin a bai wa wasu damar ba da gudunmawa.
A cewarsa:
"Wannan gurbin nasa da ya raina, wasu za su iya zuwa su ba da gudunmawar da ta fi tasa."
Ya kuma ce:
"Fitar ɗan siyasa ba daɗi ba ce, amma wani lokaci akwai abin da ake murna da shi."
'Kwankwasiyya murhu ce' — Fasaha
Yusuf Rabi'u Fasaha ya bayyana cewa Kwankwasiyya tana da ƙarfi sosai, don haka sauya shekar mutum guda ba zai iya raunana ta ba.

Source: Facebook
A cewarsa:
"Don mutum ɗaya ya fita, bai isa ya raunana Kwankwasiyya ba."
Ya ci gaba da cewa:
"Fiye da shi, waɗanda suka fi shi amfani sun fita, kuma Kwankwasiyya na nan har yanzu."
Fasaha ya ƙara da cewa abin da yake ba shi mamaki shi ne, duk wanda ya bar Kwankwasiyya yakan rasa tasirin siyasa.
A kalamansa:
"Abin burgewa shi ne duk wanda ya bar Kwankwasiyya, ya zama kamar gawa, ba shi da amfani sam."
Sanata Hanga ya shiga NDC
A baya, mun wallafa cewa Sanata Rufai Hanga ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), yana mai cewa ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari kan lamarin.
Sanatan Kano ta Tsakiya ya ce zai mayar da hankali kan wasu harkoki da manufofinsa na kashin kai bayan barin jam'iyyar bayan lokaci da aka kwashe ana buga muhawara game da sauya shekarsa.
Sanata Rufa'i Hanga ya gode wa shugabanni da mambobin NDC bisa goyon baya da haɗin kan da suka ba shi a lokacin da yake cikinta, tare da bayyana cewa amma yanzu ya hakura da ita.
Asali: Legit.ng
