Babban Sarki Ya ba Sunday Igboho Miliyoyi da Mota domin Yaki da Yan Bindiga a Dazuka
- Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ya bai wa cibiyar tsaron Iru Ekun ta Sunday Igboho tallafin miliyoyin kudi da sabuwar motar Hilux
- Sarkin ya yaba wa Sunday Igboho kan jajircewarsa wajen kare rayuka da dukiyoyin Yarbawa, yana kira ga masu ruwa da tsaki su mara wa shirin baya
- Sunday Igboho ya gode wa Ooni bisa tallafi da goyon baya, sannan ya sanar da shirin taron sarakunan Yarbawa domin tattauna hanyoyin inganta tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya ba da tallafin makudan kudi da mota ga ƙungiyar tsaro da Sunday Igboho.
Basaraken ya bayar da Naira miliyan 100 tare da sabuwar motar Hilux domin tallafa wa cibiyar tsaron Iru Ekun da ke yaki da yan bindiga.

Source: Facebook
Igboho ya ziyarci Ooni na Ife
An bayyana tallafin ne a ranar Talata yayin wata ziyarar girmamawa da Sunday Igboho da mambobin cibiyar tsaron Iru Ekun suka kai fadar Ooni da ke Ile-Ife, cewar Tribune.
A cewar sanarwar da babban jami'in yada labarai na Ooni, Sodiq Lawal, ya fitar a madadin Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama'a, Otunba Moses Olafare, sarkin ya ce an kafa cibiyar tsaron ne domin taimaka wa hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummar Yarbawa.
Ooni ya yabawa Sunday Igboho bisa jajircewarsa, juriyarsa da kuma sadaukar da kai wajen tabbatar da tsaro da jin dadin al'ummar Yarbawa.

Source: Instagram
Musabbabin ba da tallafi ga Igboho
Sarkin ya bayyana cewa tallafin kudin da motar Hilux da ya bayar alama ce ta goyon bayansa ga duk wani yunkuri da ke inganta zaman lafiya, hadin kan al'umma da kuma kare yankunan Yarbawa.
Ya ce:
"Ina yabawa Cif Sunday Igboho saboda wannan gagarumin mataki na karfafa tsaron al'umma. Kare rayukan jama'armu alhaki ne da ya rataya a wuyan kowa ba tare da la'akari da siyasa, addini ko akida ba. Duk wani shiri na gaskiya da ke kare rayuka da zaman lafiya ya cancanci a tallafa masa."
Ooni ya kuma yi kira ga fitattun 'ya'yan Yarbawa, sarakuna, shugabannin al'umma, 'yan kasuwa, kwararru da sauran masu ruwa da tsaki a fadin duniya su tallafa wa cibiyar tsaron Iru Ekun.
Ya bayyana Sunday Igboho a matsayin jajirtaccen mai kishin al'umma, yana mai cewa tarihi zai tuna da wadanda suka tsaya tsayin daka wajen kare mutanensu a lokutan kalubale, cewar Daily Post.
Abin da Igboho ya fadawa Sarki
Da yake mayar da martani, Sunday Igboho ya gode wa Ooni bisa tallafin kudi da kuma karfafa masa gwiwa da ya yi wa cibiyar tsaron Iru Ekun.
Ya bayyana Ooni a matsayin uba ga dukkan Yarbawa a duniya, yana mai cewa hikimarsa, tawalinsa da kokarinsa wajen hada kan Yarbawa suna ci gaba da zaburar da miliyoyin mutane.
Ya ce:
"Ooni uba ne ga daukacin Yarbawa a duniya. Kyauta ce daga Allah ga al'ummarmu. Soyayyarsa ga Yarbawa, tawali'unsa da kyawawan halayensa sun bambanta shi da sauran sarakuna."
Yaran Igboho sun gwabza da ƴan bindiga
An ji cewa rahotanni da suka fito daga Oyo sun nuna cewa an jikkata wasu jami'an sa-kai da ke da alaka da Sunday Igboho da suka je fafatawa da 'yan bindiga.
Tawagar tsaron Iru Ekun da ke da alaka da Igboho na gudanar da sintiri a daji ne domin gano maboyar masu garkuwa da mutane da sauransu.
Duk da yadda labarin ya bazu, zuwa yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka ji rauni ba kuma 'yan sandan jihar Oyo ba su fitar da sanarwa ba.
Asali: Legit.ng


