Malamin addini Ya Tubure kan Dokar Gwamnatin Tinubu na Hana Wa'azi, Ya Sha Alwashi
- Kungiyar PFN ta ce ba za ta daina wa'azi a motocin haya ba, ko da gwamnati ta kama mambobinta saboda sabon kudirin gyaran dokar FRSC
- Fasto Wale Oke ya ce Kiristoci za su ci gaba da wa'azi a ko'ina, yana mai cewa sun fi bin umarnin Allah fiye da dokokin da suka takaita wa'azi
- Majalisar Dattawa ta ce kudirin bai haramta wa'azi a fili ba, illa dai yana maida hankali kan kare lafiyar fasinjoji da masu amfani da hanya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wani yunkuri na hana Kiristoci yin wa'azi a motocin haya ba.
Ta jaddada cewa mambobinta za su ci gaba da yada bishara ko da an kafa doka da za ta hukunta hakan.

Source: Twitter
Fasto ya sha alwashi kan wa'azi a motocin haya
Shugaban PFN, Fasto Wale Oke, ya bayyana haka a ranar Laraba yayin wata hira da aka yi da shi a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels.
Ya yi martani ne kan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan Kudirin Gyaran Dokar Hukumar Kare Hadurra ta Kasa (FRSC) na shekarar 2026, wanda ya tanadi tarar Naira dubu 50 ga duk wanda aka samu da laifin talla, fatauci ko wa'azi a cikin motocin haya.
Fasto Oke ya ce idan gwamnati na son daure masu wa'azi saboda yin wa'azi a mota, to su shirye suke su fuskanci hakan domin ba za su daina yada bishara ba.
Limamin cocin Sword of the Spirit Ministries International ya ce Kiristoci za su fi bin umarnin Allah fiye da na mutane, yana mai cewa hana wa'azi a bainar jama'a ya saba da kundin tsarin mulkin Najeriya da ya ba kowa 'yancin bayyana addininsa.
Yana kare kalaman da ya yi a wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, Fasto Oke ya sake nanata cewa ba za su janye daga wa'azi a wuraren jama'a ba.
Ya ce idan gwamnati na son aiwatar da irin wannan doka, sai ta mayar da dukkan filayen wasa na Najeriya gidajen yari, domin Kiristoci za su ci gaba da wa'azi a motocin haya da sauran wurare.

Source: Facebook
Fasto ya magantu kan bambancin addini a Najeriya
Fasto Oke ya kara da cewa Najeriya kasa ce ta mabambantan addinai, don haka ya kamata a ci gaba da mutunta 'yancin kowa na gudanar da addininsa.
Sai dai Majalisar Dattawa ta bayyana cewa kudirin gyaran dokar bai kirkiro da sabon haramcin wa'azi ko talla a motocin haya ba.
A cewar majalisar, wannan tanadi ya riga ya kasance cikin Dokar Kafa Hukumar FRSC ta shekarar 2007, inda aka saka shi a matsayin Abu na 36 na Jadawali na Biyu, sannan aka sake adana shi a matsayin Abu na 49 a sabon kudirin.
Majalisar ta kuma yi nuni da Dokar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Kasa ta shekarar 2012, musamman Sashe na 220, a matsayin hujjar wannan tanadi.
Kiristoci sun fusata kan dokar hana wa'azi
An ji cewa kungiyar Organisation of African Instituted Churches ta shawarci Shugaba Bola Tinubu kan dokar hana wa'azi.
Ta bukaci shugaban kada ya sanya hannu kan kudirin gyaran dokar FRSC da zai hukunta wa'azi a motocin haya.
Kungiyar ta ce daidaita wa'azi da talla a cikin motocin haya ya saba da kundin tsarin mulki, saboda yana tauye 'yancin addini da fadin albarkacin baki.
Asali: Legit.ng


