Jam'iyyun Siyasa 22 Sun Cika Sharadin da Hukumar INEC Ta Gindaya kafin Zaben 2027

Jam'iyyun Siyasa 22 Sun Cika Sharadin da Hukumar INEC Ta Gindaya kafin Zaben 2027

  • Hukumar INEC ta tabbatar da cewa jam'iyyun siyasa 22 sun mika kundin rijistar mambobinsu kamar yadda dokar zabe ta 2026 ta tanada
  • Hakan ya biyo bayan kara wa'adin mika sunayen mambobin kowace halastacciyar jam'iyya da INEC ta yi a kwanakin baya
  • INEC mai zaman kanta ta ce yanzu za a fara tantance kundin rajistar da jam'iyyun siyasar suka mika bisa tanadin doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam'iyyun siyasa 22 a Najeriya sun cika sharadin da dokar zabe ta shimfida na mikawa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) sunayen mambobinsu.

INEC ta sanar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa 22 da aka yi wa rajista sun mika kundin rajistar mambobinsu domin bin tanadin dokar zabe ta 2026 gabanin babban zaben 2027.

Shugaban INec.
Shugaban hukumar zabe ta Najeriya (INEC), Farfesa Joash Amupitan yana ganawa da kwamishinoni a Abuja Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Jam'iyyu 22 sun mika wa INEC sunayen mambobi

Kara karanta wannan

Obika: Dalilin da ya sa 'dan majalisar tarayya ya canza jam'iyya sau 2 cikin watanni 2

Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kan Masu Zabe na INEC, Mohammed Kudu Haruna, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka wallafa a shafin hukumar na Facebook ranar Juma'a.

INEC ta ce mika kundin rajistar ya biyo bayan karin wa’adin da ta bai wa jam’iyyun siyasa bayan da suka nuna damuwa kan wa’adin farko a wani taro da aka gudanar ranar 24 ga Maris, 2026.

A cewar hukumar, dukkan jam’iyyun siyasar sun mika kundin rajistar mambobinsu a ranar 8 ga Mayu, 2026 ko kafin hakan, kwanaki biyu kafin cikar sabon wa’adin ranar 10 ga Mayu.

Dalilin hukumar INEC na tsawaita wa'adi

"Mun yi karin wa’adin ne bayan jam’iyyun siyasa sun nuna damuwa a wani taro da aka gudanar ranar Talata, 24 ga Maris, 2026, dangane da jadawalin da aka tsara a sabon tsarin ayyukan babban zaben 2027,” in ji sanarwar.

INEC ta tunatar da cewa bayan tattaunawa da jam’iyyun siyasa, ta sauya wa’adin mika kundin rajistar daga ranar 21 ga Afrilu, 2026 zuwa ranar 10 ga Mayu, 2026.

Hukumar ta bayyana cewa an yi hakan ne domin dacewa da tanadin Sashe na 77(4) na Dokar Zabe ta 2026 da kuma ranakun da jam’iyyun siyasa suka ware domin gudanar da zabukan fidda gwani.

Kara karanta wannan

NDC: Jam'iyyar su Kwankwaso ta fitar da kudin fom din takarar 2027

Inec.
Tambarin hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta (INEC) Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

INEC za ta fara tantance mambobi

Ta kara da cewa an bai wa jam’iyyun damar gudanar da zabukan fidda gwani tsakanin ranar 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayu, 2026, yayin da ake bukatar su mika kundin rajistar mambobinsu akalla kwanaki 21 kafin kammala zabukan fidda gwani.

INEC ta ce yanzu za a fara tantance kundin rajistar da aka mika bisa tanadin doka.

“Hukumar zabe na ci gaba da jajircewa wajen gudanar da sahihin zabe, mai gaskiya, adalci da kuma wanda zai hada kowa da kowa,” in ji sanarwar.

Hukumar INEC ta soki yunkurin soke rijistar ADC

A wani labarin, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta nuna adawa ga wani yunƙuri na soke rajistar jam'iyyar adawa ta ADC.

INEC ta ce soke rajistar kowace jam'iyyar siyasa yana ƙarƙashin jagorancin dokoki ne da tanadin kundin tsarin mulki, ba wai matsin lambar siyasa ba.

Hakan na zuwa ne bayan kungiyar tsofaffin yan Majalisu ta shigar da kara gaban kotu, tana neman a soke rijistar jam'iyyar ADC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262