Wike Ya Sha Rubdugu wajen 'Yan Arewa da Ya Taba Faston da Ya Soki Tinubu
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce Cardinal John Onaiyekan ba ya nuna taka tsantsan kan siyasa tun daga zaɓen 2023
- Ƙungiyar Matasan Arewa ta Najeriya ta kare Onaiyekan, tana mai cewa ya faɗi gaskiyar halin ƙuncin da 'yan Najeriya ke ciki
- Kungiyar Middle Belt Forum da CBCN sun kuma tsaya kan matsayinsu cewa ya kamata gwamnati ta saurari koken al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce Archbishop Emeritus na Cocin Katolika da ke Abuja, Cardinal John Onaiyekan, ba mutum ne mai taka tsantsan ba idan aka zo batun siyasa.
Wike ya yi wannan bayani ne yayin taron sa na wata-wata da manema labarai, inda ya mayar da martani kan kalaman da Onaiyekan ya yi bayan ganawarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa kalaman ministan sun haifar da martani daga Ƙungiyar Matasan Arewa ta Najeriya (NYCN) da kuma Middle Belt Forum (MBF), waɗanda suka bayyana goyon bayansu ga Cardinal Onaiyekan.
Wike ya soki Bishop Onaiyekan
Nyesom Wike ya ce duk da cewa gwamnati na buƙatar karɓar suka, ya kamata a riƙa yabawa idan ta yi abin kirki.
A cewarsa, idan mutum yana sukar gwamnati a ko da yaushe ba tare da yaba mata ba, hakan na nuna cewa yana da wata manufa ta siyasa.
Punch ta rahoto ya ce:
"Na san matsayin Cardinal Onaiyekan. Dukanmu mun san wanda yake goyon baya, ba wani sirri ba ne. Kowa ya san hakan."
Wike ya kuma yi zargin cewa shugabannin addinai da dama sun fito fili sun goyi bayan 'yan takara a zaɓen 2023, saboda haka bai dace a ce ba su da son rai ba.
Matasan Arewa sun soki Wike
A martanin da ta fitar, Ƙungiyar Matasan Arewa ta Najeriya (NYCN) ta ce Cardinal Onaiyekan ya bayyana abin da miliyoyin 'yan Najeriya ke fuskanta na tsadar rayuwa, hauhawar farashi da matsalar tsaro.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Isah Abubakar, ya ce maimakon a mayar da hankali wajen sukar malamin, ya kamata jami'an gwamnati su mayar da hankali kan magance matsalolin da ya kawo.
Ƙungiyar ta kuma yabawa Cardinal Onaiyekan bisa abin da ta kira jajircewarsa wajen faɗa wa masu mulki gaskiya, tare da kira ga sauran shugabannin addinai da na gargajiya su ci gaba da kare muradun al'umma.

Source: Facebook
MBF ta nuna goyon baya
Rahotanni sun nuna cewa Middle Belt Forum ma ta bayyana goyon bayanta ga Cardinal Onaiyekan da kuma kungiyar CBCN.
Ƙungiyar ta ce shugabannin addini suna da hakkin bayyana damuwarsu kan halin da ƙasa ke ciki, musamman idan ya shafi jin daɗin jama'a, shugabanci nagari da tabbatar da adalci.
Ta buƙaci gwamnati ta fi mayar da hankali kan magance matsalolin tattalin arziki da tsaro maimakon mayar da martani ga masu bayyana damuwarsu.
Martanin fadar shugaban ƙasa
A wani labarin, mun ruwaito cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta soki shugabannin kungiyar Bishop ta CBCN kan yadda suka bayyana bayanan ganawarsu da Shugaba Bola Tinubu.
Mai ba shugaban ƙasa shawara, Daniel Bwala, da Temitope Ajayi sun ce kalaman bishops ba su wakilci ra'ayin dukkan Kiristocin Najeriya ba.
Sun kuma bayyana cewa bayyana bayanan tattaunawar sirri da aka yi da shugaban ƙasa bai dace ba, tare da kare martanin Tinubu kan zarge-zargen da bishop suka yi.
Asali: Legit.ng


